in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na A
2010-06-21 16:37:43 cri
Masu karatu, bari mu leka asirin da ke cikin rukunnoni 8 da za su bayyana a Afirka ta Kudu a watan Yuni a wannan shekara. Babu shakka za mu fi mai da hankali kan kungiyoyin kasashen Afirka. Yau za mu nazari kan rukuni na farko, wanda kungiyoyin Afirka ta Kudu da Faransa da Mexico da Uruguay za su kara da juna.

Bisa sakamakon kada kuri'ar raba gardama da kungiyar FIFA ta yi a kan tashar intanet, an ce, masu sha'awar wasan kwallon kafa da ke da tsaka-tsakin ra'ayi da yawa na fatan kungiyar Afirka ta Kudu da ta shirya gasar za ta samu maki mai kyau a kasarsu, amma sun tausaya, saboda watakila kungiyar Afirka ta Kudu ita ce wadda ta fi samun rashin sa'a a yayin da ta shirya gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya. Gaskiya abubuwa a fili sun nuna cewa, sakamakon jefa kuri'a cikin kungiya kungiya a wannan karo ya kawo wa kungiyar Afirka ta Kudu cikkas wajen fita daga rukuni na farko. Ko da yake wasu 'yan kwallonta kaman Bernard Parker da Benni McCarthy suna wasa a kasashen Turai, amma sun kasance wadanda za a iya maye gurbinsu a cikin kulob kulob dinsu. A yayin kasaitacciyar gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya, da kyar su kai labari, amma a matsayinta na wadda ke shirya gasar, watakila kungiyar Afirka ta Kudu za ta taka rawar gani.

Ana kira kungiyar Afirka ta Kudu da sunan "Bafana Bafana" wato yara maza na Afirka ta Kudu. Carlos Parreira shi ne babban mai horas da 'yan wasa na kungiyar. Yanzu yana fuskantar matsalar jefa kwallo a ragar abokan karawa. 'Yan kwallon Afirka ta Kudu ba su gwanance wajen jefa kwallo a ragar abokan karawa ba. Duk da haka, abin farin ciki shi ne wannan dan kasar Brazil wato Parreira ya tsara dabaru daban daban na kai hari. Kuma ana sa ran cewa, a karkashin shugabancinsa, kungiyar 'yan wasan Afirka ta Kudu da ba su da isasshen kwarewar kai hari za ta samu babban canji.

Sa'an nan kada mu manta da fifikon da kungiyar Afirka ta Kudu ke nunawa, wato samun bakuncin shirya gasar. Ko da yaushe kungiyar Afirka ta Kudu ta yi gasa, 'yan kallo kan yi ta busa kakaki na Vuvuzela. Amon irin wannan kakaki na musamman yana shiga kunnuwan abokan karawar kungiyar Afirka ta Kudu. Ya kan karfafa gwiwar 'yan kwallon Afirka ta Kudu a filin wasa. Wannan ya taimakawa kungiyar Afirka ta Kudu samun nasara da ba za a iya kwatanta ta da sauran ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China