in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitaccen tarihin marigayi shugaban kasar Najeriya Alhaji Umaru Yar'Adua
2010-05-06 20:33:32 cri

Allah ya yi wa shugaban kasar Najeriya Alhaji Umaru Yar'Adua rasuwa a jiya Laraba a birnin Abuja bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Marigayi Yar'Adua ya fito ne daga jam'iyyar PDP inda a karkashin jam'iyyar ce ya samu nasarar zama shugaban kasar Najeriya a shekara ta 2007 kuma ya kasance shugaba na farko dake da ilimin digiri a kasar.

An haifi marigayin ne a cikin zuriyar dake da asali ta fuskar siyasa a Arewacin jihar Katsina a shekara ta 1951.

Haka zalika mahaifin marigayin ya taba zama minista a lokacin gwamnatin farko bayan samun yancin kan Najeriya daga turawan mulkin mallaka a shekara ta 1960 kuma a wanccen lokaci dan'uwansa ya kasasnce shi ne na biyu a kasar a lokacin da Olusegun Obasanjo ya ke rike da mukamin shugaban mulkin soji a kasar a shekara ta 1970.

Marigayi Yar'Adua ya taba zama malamin chemistry wato sanin halittu da dabarun hada magunguna kuma ya taka rawa sosai a bangaren kasuwanci daga bisani sai shiga harkokin siyasa dumu dumu a cikin shekara ta 1980.

Haka kuma ya dan yi fice a cikin kasar kafin tsohon shugaban kasar Obasanjo ya tsaida shi a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar PD.P. a karshen shekara ta 2006.

Har ila yau ya kasance shugaban kasar Najeriya na farko da ya fayyace ko kuma ya nuna kadarorin sa kuma ya kasance mai yin ta ka tsan tsan tare da nuna gaskiya da adalci wajen tafiyar da dukiyar al'umma. Haka zalika an karrama shi ta hanyar ba shi kyaututtuka saboda nuna tsoron Allah wajen tafiyar da harkokin mulkinsa yadda ya kamata..

Haka kuma a lokacin rayuwarsa ya yi kokari wajen ga no matsalolin da suka shafi yankin Niger Delta kuma yankin ya kasance wurin da ya fi ba da fifiko a kai.

Ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mata daya da yaya bakwai.

AbdulAziz Mu'azu

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China