in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Yinchuan, wani kyakkyawan birnin da aka zaba wajen zama da kuma tafiyar da a ciki yadda ya kamata
2010-03-19 17:39:58 cri

Birnin Yinchuan yana tsakiyar sararin yankin Ningxia da ke da wadatattun albarkatu, rawayan kogi ya ratsa birnin, inda kuma ake samun al'adun gargajiya masu dogon tarihi da halayen musamman na musulunci da kuma wurare masu kayatarwa. Lokacin da yake tabo magana kan garinsa, magajin birnin Yinchuan Wang Rugui ya bayyana tare da yin alfahari, cewa

"Lokacin da abokai suka zo birnin Yinchuan, za su iya ganin shudin sararin sama da farin gajimare da kuma tsuntsayen da ke tashi cikin 'yancin kai. Ban da wannan kuma ana iya samun dimbin bishiyoyi da kuma ruwan koguna da ke cikin birnin ko kuma kewayensa. A galibi dai dan Adam da muhallin halittu suna zama tare yadda ya kamata a birnin."

Gaskiya ne, kamar yadda Wang Rugui ya siffanta, sakamakon kyakkyawan muhallin halittu, a kan kira birnin Yinchuan "birnin tabki da ke arewa maso yammacin Sin". Kuma bisa kididdigar da aka bayar, an ce, yanzu fadin fadamu da ke cikin birnin Yinchuan ya kai fiye da kadada dubu 32, wanda ya kai kusan kashi 10 cikin kashi dari na dukkan yawan gonakin birnin, a ciki, yawan fadin tabki ya zarce kadada dubu 12. Birnin tabki shi ne kyakkyawan sharadi da birnin Yinchuan ya kafa don raya birnin domin ya zama birnin da ya fi dacewa wajen zama da kuma raya ayyuka a ciki.

Kuma Wang Rugui ya bayyana cewa, kyakkyawan muhallin halittu wani tushe ne wajen raya birnin, kyawawan muhimman ayyukan yau da kullum da kuma ayyukan ba da hidima su ne abubuwan da ke iya jawo hankalin mutane cikin dogon lokaci. Sabo da haka, bayan da birnin Yinchuan ya gabatar da burin raya birnin domin ya fi dacewa da yin zama da kuma raya ayyuka a ciki a shekara ta 2006, gwamnatin birnin ta sanya muhimmanci kan raya ayyukan ban ruwa da hanyoyi da dasa bishiyoyi, da kuma gaggauta raya muhimman ayyukan yau da kullum. A waje daya kuma, an mai da hankali sosai kan raya birnin Yinchuan wajen sayen kayayyaki da yin zama da yawon shakatawa da samun ilmi da kuma kiwon lafiya. Game da wadannan matakan da gwamnatin Yinchuan ta dauka, Wang Rugui ya ce,

"Muna tsayawa tsayin daka kan mayar da dan Adam a gaban kome, kuma muna ganin cewa, tabbas ne a kafa wani tsari da zai hada da dakunan kwana da samun ilmi da kiwon lafiya da inshorar tsoffi tare. Hakan bayan da aka zo birnin Yinchuan, tsoffi za su samu inshora, kuma za a iya ganin likita da samun dakunan kwana yadda ya kamata, ta yadda za a samar musu sauki sosai a fannin zaman rayuwa."

Ba kawai za a raya birnin Yinchuan domin ya dace da yin zama a ciki ba, a'a har ma birnin ya zama wani wurin da za a iya raya ayyuka sosai a ciki. Birnin Yinchua ya yi amfani da rinjayensa a matsayin garin 'yan kabilar Hui masu bin addinin Musulunci domin jawon hankalin 'yan kasuwa musulmai daga gida da waje. A matsayinsa na hedkwatar jihar kabilar Hui mai cin gashin kanta daya tak ta kasar Sin, birnin Yinchuan ya nuna fifiko sosai a fannin jawo hankalin 'yan kasuwa musulmai. Wang Rugui ya gaya wa wakilinmu cewa, sun tsara manufofin musamman a jere don 'yan kasuwa musulmai domin biyan bukatunsu a fannin zama da kuma raya ayyuka. Kuma ya fadi cewa,

"bayan da abokan kasashen musulmai suka zo birnin Yinchuan, za mu yi kokarin samar masu da masu dafa abinci da malaman koyarwa da makarantun musamman masu kayatarwa bisa al'adunsu, ta yadda za su iya samun sauki kamar yadda mazaunan birnin ke yi. A waje daya kuma idan sun zo jihar Ningxia don raya ayyukansu, to lokacin da muke aiwatar da manufofi, za mu ba da gatanci ga abokanmu na kasashen waje, ta yadda za su iyar zama da kuma raya ayyuka cikin farin ciki a birnin Yinchuan kamar yadda suka yi a gidajensu."

Ban da manufofin ba da gatanci, birnin Yinchuan shi ma ya yi amfani da wurin da yake ciki da al'adu da kuma albarkatu masu rinjaye wajen raya abinci da kayayyakin musulmi domin ya zama wata sabuwar sana'a da ke iya sa kaimi ga karuwar tattalin arzikin wurin, ta yadda za a shimfida wata sabuwar hanya ta jawo hankalin masu zuba jari. Wang Rugui yana ganin cewa, ana iya samun dimbin mutane da ke cin abincin musulmi da amfani da kayayyakin musulmi, shi ya sa sana'ar tana da kyakkyawar makoma. Kuma ya kara da cewa,

"wadannan abubuwa na kabila na da halin musamman, da ba a iya samunsu a ko ina, shi ya sa suna da kasuwa da kuma karfin takara."

Wang Rugui ya kuma bayyana cewa, lokacin da ake kaddamar da shirin raya sana'ar, gwamnatin birnin Yinchuan ta kan kebe kudade Yuan miliyan biyar a ko wace shekara domin samar da taimako a fannonin yin fasalin tufafin musulmi da sabunta kayayyaki da samun shahararrun abubuwan marmari na musulmi da kuma al'adun gargajiya na kabilar Hui. Bayan da aka raya sana'ar musulmi a tsawon shekaru da dama, yanzu sana'ar ta birnin Yinchuan ta riga ta zama wata muhimmiyar sana'a ta musamman da ke da cikaken karfi sosai. Yanzu ana fitar da abinci da kayayyakin musulmi zuwa kasashen Jordan da Libya da Malaysia da Amurka da kuma shiyyar Hongkong don cinikinsu. Wang Rugui ya furta cewa,

"Yanzu abinci da kayayyakin musulmi suna samun bunkasuwa a duk fadin kasar Sin har ma a duk duniya. Muna da tasoshin fitar da wadannan abubuwa a gida kamar biranen Shenzhen da Shanghai da Yiwu, ta haka kayayyakinmu sun kara samun shahara, kuma sun kara samun ingantuwa da amincewa. Ban da wannan kuma muna da tasoshin sayar da su a kasashen Larabawa, inda suka samu karbuwa sosai daga wajen musulman wurin."

Girman sana'ar musulmi ya jawo hankalin dimbin 'yan kasuwa wajen zuba jari a birnin Yinchuan, a yayin babban taron farko na 'yan kasuwa na kabilar Hui da aka kira a watan Satumba na shekara ta 2008 kawai, an tabbatar da ayyuka 19 na hadin gwiwar Yianchuan da kamfanonin gida da na waje, wadanda darajarsu ta zarce Yuan biliyan 50, haka kuma an daddale wata kwangilar cinikayya da jimillarta ta kai Yuan biliyan 1.86. Wang Rugui ya fayyace cewa, za a kira baban taro a karo na uku na 'yan kasuwa na kabilar Hui da kuma taron dandalin tattaunawar cinikayya a tsakanin Sin da kasashen Larabawa a birnin Yinchuan a bana, wanda zai jawo hankalin 'yan kasuwa na kasashen musulmai wajen zuba jari a birnin Yinchuan. Ya ce,

"Muna kokarin shirya taron tattaunawar cinikayya a tsakanin Sin da kasashen Larabawa a birnin Yinchuan, da kuma kira taron 'yan kasuwa na kabilar Hui a karo na uku domin jawo hankalin 'yan kasuwa na gida da na kasashen musulmai wajen zuba jari a Yinchuan, da kuma fitar da abinci da kayayyakin musulmi na Yinchuan zuwa ketare, ta yadda tattalin arzikinmu zai kara samun bunkasuwa, jama'ar birnin kuma za su samun muradu sosai."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China