in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dilnar Abdullah, yarinyar da aka haife ta domin rawa
2010-03-19 16:22:06 cri

Idanunta na iya magana, kuma ga ta sirirriya. Ita ce yarinyar da aka haife ta domin rawa, kuma wakiliya ce ta wakilan jama'ar kasar Sin kuma shugabar kungiyar masu rawa ta jihar Xinjiang, wacce aka san ta da suna Dilnar Abdullah.

A shekarar 1966, an haifi Dilnar Abdullah a birnin Urumqi, hedkwatar jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Mahaifinta shi ne shugaban sashen kula da wakoki na kungiyar masu rawa da mawaka ta jihar Xinjiang, kuma mahaifiyarta wata mai rawa ce cikin kungiyar. Sabo da haka, Dilnar ta girma ne cikin wannan yanayi, har ma ta ba mahaifinta mamaki lokacin da ta gwada rawa a lokacin da take da shekaru hudu kawai. A lokacin da take da shekaru shida da haihuwa, Dilnar ta iya kidan Duttar a yayin da take waka, abin da ya faranta wa mahaifinta rai sosai.

Dilnar ta ce, "da farkon fari, mahaifiyata tana so in koyi waka a maimakon rawa." Ta kara da cewa, "kasancewarta mai rawa, mahaifiyata ta san wahalar wannan sana'a. Amma duk da haka, burina shi ne in zama mai rawa." Rashin amincewar da mahaifiyarta ta nuna bai ko rage kaunar rawa da Dilnar ke yi ba. Lokacin da ta gama karatun firamare, sashen koyon fasahohi na kwalejin kabilun kasar Sin ya fara daukar dalibai a jihar Xinjiang, da Dilnar ta sami labarin, sai ta shiga jarrabawar da aka yi, har ma ta ci jarrabawar da maki mai kyau. Yadda Dilnar ke kaunar rawa ya burge mahaifiyarta. Lokacin da mahaifiyarta ke ban kwana da ita a tashar jiragen kasa, ta ce mata, "ke ce kika zabi rawa, to, sai ki yi kokari ki zama mafi gwaninta, in ba haka ba, kar ki tafi." Da haka, Dilnar ta kama hanyar zuwa birnin Beijing domin koyon rawa.

Yayin da take karatu a jami'ar kabilu ta kasar Sin, Dilnar Abdullah ta kan yin kokarin karatu kamar yadda mahaifiyarta ta gaya mata. Yayin da abokan karatunta suka yi sa'a guda wajen gwajin jiki, ita ma, ta kan yi sa'o'i 3. kana, domin kokarin ganin ta motsa jiki, har ma yayin da Dilnar take barci, ta kan yi kokarin motsa jikinta. A ko wace rana, kafin a shiga darasi, Dilnar ta kan sa jakar rairaiyi da nauyinta ya kai kilogram 2 a kafafunta, ta kan yi gudu a filin wasannin motsa jiki har zagaye 30, sa'an nan ta kan je aji.

Ban da kokarin motsa jiki, Dilnar ta kan lura sosai wajen fahimtar ma'anar raye-raye kuma ta ce, 'raye-raye ba wai yana nufi mu yi tsalle-tsalle ne kawai ba, amma dole ne mu yi mu'amala da 'yan kallo ta ido, kuma mu sake fuska.'

Bayan da Dilnar ta fahimci wannan, sai ta kware a ko wane salon raye-raye, kamarsu raye-raye na kabilar Mongolia da na Kazak da na Uygur.

A shekarar 1982, Dilnar ta kammala karatu a jami'ar kabilu ta kasar Sin. Ko da yake mahukuntan makarantan sun gayyaci Dilnar da ta zama malama a makaranta har sau da dama, amma Dilnar ta nace ta koma garinta---jihar Xinjiang, Ta ce, 'sabo da jihar Xinjiang ta yi nisa da birnin Bejing, ba wai ko wane mutum zai iya samun damar koyon wasannin raye-raye a birnin Beijing ba. Sabo da haka, ya zama dole na koma jihar Xinjiang, domin kawo irin abubuwan da na koyo a nan birnin Beijing zuwa Xinjiang, da kara raya fasahohin raye-raye na jihar Xinjiang. Sabo da jihar Xinjiang na bukatanmu.'

Bayan da ta koma jihar Xinjiang, Dilnar ta zama 'yar wasannin rawa a kungiyar kide-kide da raye-taye ta jihar Xinjiang. Bayan shekaru 3, yayin da shekarunta suka kai 18, sai ta shirya wasannin raye-raye da kanta, daga wancan lokaci, ta samu lambobin tabo da dama da karbuwa a wajen jama'a. Ko da yake ta samu lambobin yabo na zinariya da dama a cikin gida da kasashen waje. Amma har yanzu, ba za ta manta da halin da ake ciki ba, yayin da take halartar wasannin a karo na 1 kan fasahohin raye-raye na Olympic na duniya da aka yi a kasar Koriya ta kudu a shekarar 2004. Sabo da tana kokarin motsa jiki, kafin a fara yin wasanni, Dilnar ta samu raunuku a gwiwowinta, har ma tana shan wahalar tafiya, amma yayin da aka nuna kide-kide na 'Yarinyar Dabancheng', sai ta manta da radadi da take ji, inda 'yan kallo suka yi ta mata tafi har sau fiye da 10, kuma Dilnar ta kara karfafa zuciyarta. A karshe dai, ta samu lambobin yabo na 'Shimfida zaman lafiya a duniya'. Bayan da shugaban kwamitin shirya wasannin ya fahimci cewa Dilnar ta yi rawa duk da raunin da take fama da shi, hakan ya burge sosai game da rawar da Dilnar ta yi da karfin tunaninta, amma Dilnar ta ce, 'Na gode, sabo da kana sha'awar wasannin raye-raye na kasar Sin.

Yi raye-raye ga jama'a na kananan sassa ya fi da ma'ana

A 'yan shekarun da suka wuce, Dilnar ta yi suna a fannin rawa a duniya, wasu kungiyoyin fahasa na kasashen waje sun yi fatan rike ta tare da biyan kudi da yawa, amma ta ki amincewa da su. A cikin gida kuma, ba ta taba yin wasan kwaiwayo na kwangila ba. Dilnar tana ganin cewa, jama'a na kananan sassa sun fi fama da wahalhalu, saboda haka, yin raye-raye gare su na da matukar ma'ana.

Kawo alheri ga zamantakewar al'umma

A shekarar 2006, Dilnar ta kafa wani asusu don yin musayar al'adu da fasaha a jihar Xinjiang, tana fatan taka rawa wajen tanadi da inganta al'adun raye-raye na jihar Xinjiang irin na cudanyar kabilu da dama. Dilnar ta ce, 'an kafa babban tushen al'adu a jihar Xinjiang, al'adun jihar Xinjiang na bukatar samun bunkasuwa. A matsayina na shugabar majalisar kwararru a fannin raye-raye, kamata ya yi na bayar da taimako kan sha'anin al'adu na jiharmu.'

Bayan da ta kafa wannan asusu, Dilnar ta kafa wani kwas din kara ba juna sani bisa shahararrun masu raye-raye daga kabilu guda 6, ciki har da kabilun Han, da Uygur, da Kazak, da dai sauransu. Ban da wannan kuma, ta kafa wani kwas na fasaha, don horar da tsofaffi, ta yadda za a arzuta zaman rayuwarsu. Dadin dadawa, Dilnar ta kafa wata kungiyar fasaha ga yaran da suke da sha'awar raye-raye na jihar Xinjiang. Ko da yake wadannan ba manyan abubuwa ba ne, amma sun nuna amincewar da Dilnar take nunawa ga bunkasuwar al'adun jihar Xinjiang.

Ba da shawara kan aikin raya al'adu da wasan fasaha na jihar Xinjiang

A matsayin wata wakiliyar jama'a a fannin wasan fasaha ta karamar kabila ta kasar Sin, a cikin shekaru 8 da suka gabata, Dilnar Abudullah ta yi ta nuna kulawa ga sha'anin bunkasuwar al'adu da wasan fasaha na jihar Xinjiang. Jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kasance tamkar gidan wake-wake da raye-raye, amma irin kayayyakin da dakunan da kungiyar wake-wake da raye-raye ta jihar take da su ba na a zo a gani ba ne, hakan ya kawo mummunan tasiri ga bunkasuwar sha'anin al'adu da wasan fasaha na jihar. Sabo da haka, a gun taro na 10 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Dilnar Abudullah ta ba da shawarar kara gina manyan ayyukan yau da kullum na al'adu a jihar Xinjiang, wadda gwamnatin kasar ta dora muhimmanci sosai a kai. A shekarar 2007, an kammala gina dakin wasan fasaha na jihar Xinjiang, ta haka, an kyautata halin da 'yan wasan fasaha na jihar Xinjiang suke ciki domin nuna wasannin kwaikwayo da samun horaswa. Dilnar Abudullah ta ce, "bayan da aka kammala gina dakin wasan fasaha na jihar Xinjiang, muna da kyawawan ofisoshi da dakunan horaswa, 'yan wasan fasaha na jihar sun kara sa himma kan ayyukansu, yanzu, dukkan 'yan wasan fasaha suna kokarin raya al'adu da wasan fasaha na jihar Xinjiang."

Akwai kabilu 47 a jihar Xinjiang. A cikin dogon lokacin da ya gabata, 'yan kabilu dabam daban sun kirkiro kayayyakin al'adun gargajiya na kabilunsu. Wadannan kayayyakin al'adun gargajiya suna da muhimmiyar ma'ana wajen yin nazari kan wayewar kan dan Adam da sauyawar muhalli da bunkasuwar kimiyya da fasaha da kuma musanyar al'adu dake tsakanin kabilu dabam daban na ciki da na waje. Sabo da haka, Dilnar Abudullah tana mai da hankali sosai kan aikin kare kayayyakin al'adu na gargajiya na jihar Xinjiang. A gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na shekarar 2008, ta bayar da shawarar gina dakin ajiye kayayyakin al'adu na gargajiya a jihar Xinjiang. Ta ce, "Jihar Xinjiang tana bukatar wani dakin ajiye kayayykin al'adun gargajiya, inda ya kamata a tattara wasannin fasaha na jihar Xinjiang ciki har da wasan fasaha na "Mukam" na kabilar Uygur domin gabatar da su a gaban jama'a. Wadannan kayayyakin al'adu na gargajiya masu daraja sun zama wawani muhimmin bangare daga cikin al'adun kasar Sin, kana sun zama tamkar wata muhimmiyar alama ce ta dinkuwar kasar Sin waje daya da kuma kasa mai yawan kabilu."

Kaunar iyali

A matsayinta na 'yar wasan kwaikwayo a mataki na farko kuma mataimakiyar shugaban kwamitin 'yan wasan raye-raye na kasar Sin kuma babbar malama ta jami'ar kabilu ta tsakiya ta kasar Sin, Dilnar Abudullah ta kan yi aiki sosai. Amma idan tana da lokaci, Dilnar Abudullah ta kan buga waya ga iyalinta, domin mayar da hankali kan aikin mijinta da karatun 'yarta, kana ta kan gaya musu nasarar da ta ci a aiki. A yayin da take zance kan iyalinta, ta yi farin ciki cewa, "na yi ta yin kokarin aikin raye-raye, amma ban da aikina, ni wata uwar gida kuma uwa ce, ya kamata na kula da maigida da diyarta. A matsayin mace, ina da nauyin zama uwar gida da uwa ta gari. In ba haka ba, ko da yake na cimma nasara wajen aiki, amma 'yar ba ta zama mutumiya ta gari ba, ni ba wata mace ta gari ba."

Dilnar Abudullah ta bayyana cewa, ma'anar sunanta shi ne wutar zuciya, wanda ya siffanta yadda take kokarin aiki da taimakawa sauran mutane da ba da shawara da kuma kaunar iyalinta.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China