in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abdulla Abbas, dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin
2010-03-17 16:43:08 cri

A yayin tarurrukan majalisu biyu, mun kai ziyara ga Abdulla Abbas, dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wanda kwararre ne sosai dan kabilar Tatar, inda ya bayyana zaman rayuwarsa na yau da kullum.

An haifi Abdulla a wani iyalin kabilar Tatar da suka baiwa samun ilmi muhimmanci

Kabilar Tatar wata karamar kabila ce daga cikin kananan kabilu 13 da suke zaune daga zuri'a zuwa mata a jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta, yawan 'yan kabilar bai wuce 4800 kawai ba. Ko da yake babu mutane da yawa a cikin kabilar, amma kabilar Tatar ta zama kabilar da ta fi mayar da hankali kan ilmintar da mutane a cikin kananan kabilu 56 na kasar Sin.

An haifi Abdulla Abbas a shekarar 1951 a cikin wani iyalin kabilar Tatar dake jihar Xinjiang. Abdulla ya gaya mana cewa, tun lokacin kuruciyarsa, iyayensa suka soma horar da shi ka'in da na'in, saboda haka, Abdulla ya kan shiga matsayin gaba kan karatu tun daga firamare har zuwa jami'a.

Bayan da ya gama karatu a jami'a, jami'ar Xinjiang ta yi fatan rike shi ya zama malami a cikinta. Abdulla ya ce, 'Mahaifiyata ta gaya mini cewa, yanayin malami kamar misalin wutar kandir yake, ko da yake yana kone kansa, amma ya ba da haske ga kewayensa. A ganina, ko da mutum yana da ilmi sosai, idan bai ba da ilmi ga wasu ba, to, rayuwarsa ba ta da ma'ana.' Saboda haka, Abdulla ya soma aikin ba da ilmi har na tsawon shekaru 33.

Tsirran kauci wani nau'in halitta ne na musamman, wanda yake rayuwa tare da laimar kwadi cikin dogon lokaci, har ma sun zama abu daya. Ana iya samun kauci a ko ina, kamar hayin duwatsu da jikunan bishiyoyi da kasa.

A shekarar 1990, Abdullah ya fara nazarin ilmin tsirran kauci a jihar Xinjiang saboda a da babu wanda ya taba nazarin wannan fanni a wannan jiha. Abdullah ya bayyana cewa, a nan kasar Sin, ba a mai da hankali sosai kan ilmin tsirran kauci ba. A shekarar 1980, kasar Sin ta yi taron kara wa juna sani a karo na farko kan ilmin laimar kwadi da na kauci. Tun daga can kasar Sin ta fara gudanar da ayyukan da suka shafi tsirran kauci. In an kwatanta ta da kasashe masu sukuni da suka soma nazarin tsirran daga karni na 16, kasar Sin ta kasance baya sosai. Amma wannan shi ne dalilin da ya sa ya kaddamar da nazarinsa na wadannan tsirran musamman. A ganin Abdullah, kawo yanzu kasar Sin tana binciken albarkatun da take da su. Ta haka ya kamata masu nazarin kimiyya na kasar Sin su yi kokari a fannonin da kasarsu ta gaza.

Haka zalika, Abdullah ya nuna cewa, yana fatan zai iya horar wa kasar Sin karin kwararru masu ilmin tsirran kauci, tare da samun karin bayanan da suka shafi nazari. Ya ce, ko da yake yanzu wasu kalilan din mutane ne suke nazarin tsirran kauci, ilmin tsirran kauci bai jawo hankali sosai ba, amma a sanadiyyar muhimmancin da gwamnatin Sin ke kara dorawa a kai sannu a hankali, ya yi imani da cewa, za a samu karin kwararru. Ta haka ya dauki alhakin horar wa kasar Sin, kasar haihuwarsa kwararru masu ilmin tsirran kauci.

Sabo da har yanzu kasar Sin tana kan matakin farko wajen nazarin ilmin kauci, ba a da isassun takardu da ke magana game da ilmin kauci da ake bukata ba. Farfesa Abdullah Abbas ya taba hawan babban tsaunin Kala Kunlun da tsayinsa ya kai mita 5050 daga leburin teku domin kokarin samun ainihin ilmi da ire-ire da samfurori da surori irin na kauci. Ya zuwa yanzu, an riga an gano ire-iren kauci da yawansu ya kai fiye da 400 a yankin Xinjiang. A cikin shekaru 20 da suka gabata da yake nazarin kauci, farfesa Abdullah Abbas ya rubuta bayanai fiye da 100 game da ilmin kauci, har ma ya wallafa wani littafi mai lakabi "Kaucin da ke yankin Xinjiang". Yanzu wannan littafi yana da muhimmanci sosai ga aikin nazarin ilmin kauci a kasar Sin a nan gaba.

Sakamakon haka, farfesa Abdullah Abbas ya samu yabo daga kasashen duniya. Mr. Teuvo Ahti, shugaban kungiyar masu nazarin ilmin kauci ta kasashen duniya ya yaba masa da cewa, "Kungiyar da ke karkashin jagorancin farfesa Abdullah Abbas ta shafi shekaru da yawa tana nazarin kauci a manyan tsaunukan Tianshan da Alta da Kunlun, kuma ta samu kyakkyawan sakamako da kuma bayar da bayanai da littattafai da yawa. Wasu sakamakon da suka samu sun zama sakamako na farko a fannin nazarin ilmin kauci a duniya."

A cikin shekaru da yawa da suka gabata, wasu hukumomin kimiyya da fasaha na kasashen waje sun gayyaci farfesa Abdullah Abbas da ya yi aiki a hukumominsu, amma ya ki amincewa da gayyatarsu. Farfesa Abdullah ya ce, "kasashen da suka samu ci gaba sun dade suna nazarin ilmin kauci. Kuma na'urorin da suke amfani da su na'urorin ne zamani, har ma suna da fasahohin zamani wajen nazarin wannan ilmi. Amma ina tsammanin cewa, ni Basine ne, na samu ilmi a kasar mahaifana, ya kamata ke nan na bauta wa kasarmu."

Yin namijin kokarin wajen amfani da dukkan lokaci domin bauta wa jama'a

Sabo da yana kokarin aikin koyarwa da yin aikin nazari tare, farfesa Abdullah Abbas ba shi da isashen lokaci. Duk da haka, a matsayin dan majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin tun daga shekarar 2003 har zuwa yanzu, bi da bi ne farfesa Abdullah ya gabatar da takardun ba da shawara fiye da 80 a gun manyan tarurrukan shekara-shekara na majalisar. A kan tambaye shi cewa, kullum kana shan aiki, yaya kake samun lokacin nazarin batutuwan da suke jawo hankalin jama'a? Farfesa Abdullah ya ba da amsa cewa, "ina amfani ne da kowane minti."

A ganin Abdullah Abbas, wakilin jama'a yana kasancewa tamkar kakakin jama'a. Sabo da haka, nauyi mafi muhimmanci da aka dora masa shi ne gabatar wa gwamnatin tsakiya da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke rike da karagar mulkin kasar Sin ra'ayoyin jama'a da bukatun da jama'a suke da su. "Ko da yake, ina shan aiki sosai, amma idan na tsara shiri da kyau, kuma na yi amfani da kowane minti, ko shakka babu, na iya sauke nauyin da ke bisa wuyana." Farfesa Abdullah ya ce, "lokaci yana kasancewa tamkar ruwan da ke cikin soso, idan ka matsa wannan soso, ruwa yana fitowa."

Sabo da haka, farfesa Abdullah ya matsa lokaci domin neman ra'ayoyin jama'a da matsalolin da suke fuskanta. A cikin shekaru 8 da suka gabata, ya gabatar da kyawawan shawarwari da yawa da ke da nasaba da aikin ba da tarbiyya da na tabbatar da ingancin muhalli da na kare al'adun al'ummomin kasar da dai makamatansu.

A gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi a wannan shekara, Abdullah Abbas ya gabatar da shawarar "kiyaye yanayin hamada da dausayi da ke yankin Tarim tare da magance kwararowar hamada". A cewar Abdullah, a yayin da yake nazari a yankin kudancin jihar Xinjiang, ya gano wasu sassan kogin Tarim sun bushe, har ma dazuzzukan da ke gabobin kogin sun mutu, abin kuma da ya bakanta masa rai sosai. "Dajin da ake sani da suna diversifolious poplar da ke yankin Tarim yana daya daga cikin irin wadannan dazuzzuka mafi girma a duniya, kuma idan muhallin wurin ya ci gaba da lalacewa, abin zai haddasa illoli ga muhallin garuruwa masu dausayi da ke makwabtaka da kwarin Tarim." Da lafazi mai karfi ne Abdullah ya ce, "dole ne a kara kiyaye muhalli, sabo da kiyaye muhalli shi ne kiyaye kasancewar karin rayuka a duniya." A matsayinsa na dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin daya tilo daga kabilar Tartar, ko da yake Abdullah yana mai da hankali kan kiyaye al'adun kabilar Tartar. A ganinsa, tarihi da al'adu su ne abubuwan da suka fi muhimmanci wajen fahimtar wata kabila. Yanzu haka yawan 'yan kabilar Tartar ya ragu daga 6000 a yau shekaru da dama da suka wuce har zuwa 4800, sabo da haka, tilas ne a kiyaye tarihi da al'adu na kabilar ba tare da bata lokaci ba. Sabo da haka, a shekarar da muke ciki, Abdullah ya gabatar da shawarar "kafa cibiyar kiyaye al'adun gargajiya na kabilar Tartar da ba na kayayyaki ba da aka gada daga kaka da kakanni ba a birnin Urumqi". Ya ce, "Idan aka kafa cibiyar, za ta janyo dimbin masu yawon bude ido da masana na gida da na waje, abin da zai taimaka kwarai da gaske wajen yada al'adun Tartar." Ban da kabilar Tartar, Abdullah yana kuma mai da hankali a kan ci gaban kabilu daban daban da ke jihar Xinjiang. Ya kan ce, "ni wakili ne na jama'ar kasar Sin, kuma ina wakiltar 'yan uwa na kabilu 56. Da ci gaban kasarmu, da ci gaban kabilu daban daban."

Yanzu an kammala manyan tarurruka biyu, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, Abdullah Abbas shi ma ya koma jihar Xinjiang, inda ya ci gaba da koyarwa da yin nazari. A sa'i daya kuma, ya ci gaba da sauraron ra'ayoyin jama'a, don gina wata gada tsakaninsu da gwamnati.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China