Amanbayi Dawuti ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan da suka gabata, sakamakon kara dora muhimmanci kan muhallin halittu da gwamnatin kasar Sin ta yi, halin muhallin halittu ya samu kyautatuwa sosai, kuma cibiyarsa ta samu na'urorin sa ido kan muhallin halittu na zamani. Amma sabo da haka, an kara ayyuka masu dimbin yawa ga ma'aikatan hukumomin kiyaye muhallin halittu, ko da yaushe su kan sha aiki kwarai da gaske. Don haka ya ba da shawarar cewa, ya kamata a kara yawan ma'aikatan. Ya ce,"Yanzu abin da ya fi tsanani a gabanmu shi ne karancin ma'aikata masu aikin kiyaye muhallin halittu. Sakamakon rashin albashi mai yawa, daliban da suka gama karatu daga jami'o'i ba su son zuwa kananan hukumomin kiyaye muhallin halittu don yin aiki. Don haka na ba da shawarar cewa, ya kamata a kara kebe kudi ga kananan hukumomin domin samun sabon jini a wannan fanni."