in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a yi amfani da albarkatun yawon shakatawa wajen raya gundumar Tashkurghan, in ji Dilimaolati Ibrahim, musulmi dan kabilar Tajik
2010-03-13 21:39:44 cri

Kabilar Tajik wata karamar kabila ce ta kasar Sin da ke bin addinin Musulunci, 'yan kabilar suna zama a gundumar Tashkurghan mai cin gashin kai da ke bisa tudun Pamirs a jihar Xinjiang. A matsayinsa na wakilin 'yan kabilar Tajik daya tak, Dilimaolati Ibrahim, shugaban gundumar Tashkurghan ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan da suka gabata, gundumar ta samu babban sauyi. Sakamakon shimfida hanyar mota, gundumar ta kara tuntubar sauran wurare na gida da na waje. Gundumar kuma ta zama wata gunduma da ke da tasoshin cinikin waje uku, wato suka hada da kasashen Pakistan da Afghanistan kana da yankin Kashmir da ke kasar Indiya. Bugu da kari kuma, Dilimaolati Ibrahim yana son yin amfani da wadannan tasoshin uku da kuma albarkatun yawon shakatawa wajen raya gundumar Tashkurghan. Ya kara da cewa,"Ina son amfani da tasoshin cinikin waje domin raya sha'anin yawon shakatawa don kasashen da ke makwabtaka da gundumarmu, su rika kawo mana ziyara ta kwanaki uku ko ta kwanaki bakwai, ta haka za mu samu wata kyakkyawar damar samun yawan masu yawon shakatawa."(Kande Gao) 
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China