Malam Adulla ya furta cewa, yayin da yake yin bincike a kudancin jihar Xinjiang, ya gano cewa, ruwa ya kare a wani yanki na kogin Tarim, bishiyoyi masu dimbin yawa da ke kewayen hamadar Tarim sun mutu, adun da ya haddasa kwararowar hamada, da kuma tsanantar yanayin biranen da ke kusa da hamadar. Ban da wannan kuma, sakamakon karancin kirare, manoma da ke zama a kewayen hamadar sun sare bishiyoyi da yawa, wanda ya tsananta halin da hamadar Tarim ke ciki. Don haka Abdulla Abbas ya ba da shawarar kiyaye muhallin halittu na wurin domin hana kwararowar hamada. Ya ce,"Ya kamata a yi amfani da ruwan da ke cikin matarin ruwa wajen yin ban ruwa ga bishiyoyi, da kuma hana a raya gonaki marasa amfani ba bisa doka ba. A waje daya kuma ya kamata a aika da iskar gas zuwa ko wane gidan manoma da ke kewayen hamadar Tarim, ta yadda za a iya kyautata zamansu da kuma kiyaye muhallin halittu."(Kande Gao)