in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halida Nurmamat, musulma 'yar kabilar Uzbek ta ba da shawarar kafa dokar kasuwanci ta kasar Sin
2010-03-11 21:43:32 cri

Kabilar Uzbek wata karamar kabila ce ta kasar Sin da ke bin addinin musulunci, 'yan kabilar da yawansu ya kai dubu 14 na duk fadin kasar Sin suna zama a jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar. A matsayinta ta wakiliyar 'yan kabilar daya tak a kasar Sin, Halida Nurmamat, mataimakiyar mai sa ido kan hukumar kasuwanci ta jihar Xinjiang ta dora muhimmanci sosai kan sha'anin kasuwanci. Ta bayyana cewa, ana fatan kasar Sin za ta iya fitar da dokar kasuwanci tun da wuri domin daidaita da kuma tsara tasoshin kasuwanci na duk fadin kasar.

Madam Halida ta nuna cewa, saurin bunkasuwar zaman al'umma na zamani ya kara muhimmancin tsarin tasoshin kasuwanci. Don haka ta ba da shawarar kafa doka don tsara birane musamman ma tasoshin kasuwanci. Kuma ta kara da cewa,"bayan kafuwar dokar kasuwanci, za a iya daidaita tsarin birane da kasuwanin da kuma kamfanoni. Dokar kasuwanci za ta shafe fannoni daban daban da ke da nasaba da zaman rayuwar jama'a. Ban da wannan kuma bayan kafuwar dokar, za a kyautata sufurin kayayyaki da ayyukan ba da hidima."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China