in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa 'yar kabilar Uzbek
2010-03-11 16:49:37 cri

"Ni ce wakiliya daya tak ta al'ummar Uzbek, sa'an nan na tsaya kan manufar hada kan al'ummomin kasar Sin", in ji Fatima Mahmmuti, wata mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa 'yar kabilar Uzbek

An haife ta cikin iyalin da ya kunshi kabilu daban daban

An haifi Fatima Mahmmuti a jihar Xin'jiang inda kabilar Uygur ke cin gashin kanta. mahaifinta wani soja ne dan kabilar Uygur, sa'an nan, mahaifiyarta wata 'yar kabilar Hui ce kuma ba ta taba samun damar shiga makaranta ba. Yadda take zama a kan makeken filin ciyayi tun yarintakarta, ya sa ta kan yi abubuwa a fili ba tare da boye-boye ba, wato ta samu wadatar zuci, kamar yadda ta fada. A cikin iyalinta, mahaifi da mahaifiyarta sun zo daga kabilu daban, shi ya sa al'adarsu ta fuskar zaman rayuwa sun sha bamban, har ma su kan gamu da matsala wajen yin magana da juna lokacin da suka fara aurensu. Amma, duk da haka, kowa da kowa zai iya ganin irin kaunar da take a tsakaninsu.

Sa'an nan, ganin dangantaka mai kyau da ke tsakanin iyayenta, ya sa ta magance ra'ayin kin jinin juna da a kan samu a tsakanin al'ummomi daban-daban.

Madam Fatima ta ce, 'mahaifina ya san harsunan Uzbek da Rasha, yayin da mahaifiyarta kuwa sai Sinanci kawai take iyawa. Harshensu ba daya ba ne, amma suna zama tare cikin jituwa. Yanzu na iya zama tare da mutanen al'ummomi daban daban, ba tare da jin kasancewar wata katanga a tsakaninmu ba. Hakan, a ganina, yana da alaka da tarbiyyar da na samu a wajen iyayena.'

Kafin ta girma ta yi niyyar zama wata lauya

Bayan da Fatima Mahmmuti ta gama karatun shari'a a jami'ar Xinjiang a shekarar 1985, ta dauki sana'ar lauya. Sa'an nan, ta koma yankin Tacheng, inda aka haife ta, inda ta zama wata lauya da ke aiki a cikin wani ofishin lauyoyi da gwamnati ta ware kudi ta kafa. Kamar yadda Madam Fatima ta gaya wa manema labaru cewa, 'sauran abokan karatuna 42 da suka taba karatu tare da ni a aji daya dukkansu sun zama alkalai da kuma masu gabatar da kara, sai ni kadai ce na zama lauya.' A shekarar 1997, Madam Fatima ta yi murabus daga ofishin lauyoyin, sa'an nan ta hada karfi da wani don kafa wani ofishi na kansu. Bayan wasu shekaru kuma, ta kafa ofishi na kanta, har ma ta sanya wa ofishin sunanta.

Warware rikicin kabilu, tare da kiyaye hadin kai tsakaninsu

Akwai kabilu 47 suna zama a jihar Xinjiang, a matsayinta na wata lauya ta kananan kabilu, Madam Fatima Mahemuti ta fahimta muhimmancin aikinta sosai. Tana ganin cewa, tana da nauyin kiyaye hadin kai tsakanin kabulu daban daban.

A watan Satumba na shekarar 2009, Madam Fatima ta dauki nauyi na batun yiwa mutum rauni da gangan, wanda aka zarga da laifi shi ne 'dan kabilar Han wadda ke da rinjeya a kasar Sin, sannan wanda ya yi rauni shi ne 'dan kabilar Uyghur. Mutanen biyu sun samu rashin jituwa saboda ba su fahimtar harsunan juna, haka kuma wanda ake zargi da laifi ya yi wa wani daban rauni da wuka. Dangin wanda ake zargi da aikata laifi ya sami Madam Fatima wadda ke da ilmin warware rikicin da ke tsakanin kabilu daban daban, sun nuna bakin ciki ga wanda ya yi rauni, kuma sun yarda su biya diyya kan laifin da 'dan uwansu ya aikata. Madam Fatima tana ganin cewa, wannan batu yana da muhimiiyar ma'ana a halin da ake ciki a lokacin, wannan batu ya shafi huldar da ke tsakanin kabilu. Ya kamata a daidaita wannan batu bisa ka'idar kiyaye hadin kai da ke tsakanin kabilu, kada a sa wannan batu ya kara tsananta, kuma kada a bata moriyar da ake ci na mutumin da ya yi rauni.

Fatima ta taba kai ziyara wajen iyalin mutum da aka raunana a matsayinta ta lauya sau shida, yayin da ta isar da rokon gafarar ga mutumin da ya kai kara, da burin daukan nauyin biya kudin fansa, kuma ta yi kokari wajen kare ikon mutumin da aka raunana, don neman samun sakamakon da bangarorin biyu za su amince da shi. Bisa wannan batu, Fatima ta kara neman sanin dalilin da yake sa ana samun rikicin kabilu shi ne rashin fahimta juna, idan ba a iya kawar da wannan batu ba, zai kawo illa sosai ga al'ummar kasar. Game da warware wadannan batutuwa, lauyoyin kananan kabilu sun fi lauyoyin na kabilar Han wajen yin musanya da hana tada rikici da kawar da rikicin al'umma. Ta bayyana wa manema labaru cewa, nauyin da lauyoyin na kananan kabilu suka daukar ya fi mihimmanci, sabo da haka, ya kamata lauyoyin kananan kabilu su kara taka muhimmiyar rawa wajen warware wadannan batutuwa.

A da, fatima wata lauya ce mai ba da hidima a fannin dokoki, yanzu ita wata mamba ce ta majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, ya kamata ta dauki nauyin shiga siyasa. Fatima ta bayyana cewa, bayan ta zama mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, ta nuna cewa nauyin da ke kanta ya karu. A da, a matsayinta ta lauya, ta samar da hidima a fannin dokoki kawai, ba ta yi la'akari mai yawa ba. Amma yanzu ta zama mambar majalisar, ta iya gudanar da aikinta da kyau.

Fatima ta bayyana cewa, bayan na kammala wannan batu, to zan yi la'akari sosai da dalilin da ya janyo abkuwarsa. A sa'i daya kuma, ta rubuta abin da ta yi la'akari da shi da kuma samar wa hukumomin da abin ya shafa don gudanar da alhakin da ta dauka a matsayin wata mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin. Ban da haka kuma, ta gudanar da ayyuka da yawa a fannin yin bincike, don share fage ga shawarar da ta samar.

Fatima ta bayyana cewa, tana fari ciki sosai, sabo da gwamnatin ta mai da hankali kan shawarwarin da ta gabatar, a ganinta ta dauki nauyin da ke kanta a matsayinta ta mambar majalisar wajen gabatar da shawarwari.



Nuna godiya ga kasarta da ta ba ta horo

Malama Fatima ta bayyana cewa, a matsayin tana mace ta karamar kabilar kasar Sin, idan tana dogara da karfinta kawai, za ta zama wata lauya kawai. Dalilin da ya sa ta samu babbar nasara shi ne horar da kasar ta yi mata da kuma manufofin kabilu da kasar ke aiwatar. Ta ce, a matsayin 'yar karamar kabila, ta iya shiga ayyukan siyasa a majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar tare da sauran fitattun kwararrun kabilu daban daban na kasar, ta gano gaskiyar manufofin kabilu na kasar. A ganin malama Fatima, manufofin kabilu na kasar Sin sun fi kyau bisa na sauran kasashen duniya. Ta bayyana wa 'yan jarida cewa, 'yan iyalinta da dangoginta masu yawa suna zaune a kasar Uzbekistan, lokacin da suka san malama Fatima ta zama wata memba ta majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a matsayin wata lauya ta karamar kabila, sun yi mamaki sosai, kana sun nuna yabo ga manufofin kabilu da Sin ke aiwatar.

Yin kokarin tabbatar da kare hakkin mata 'yan kananan kabilu

Ranar 8 ga watan Maris na bana ita ce ranar cika shekaru 100 da kafa ranar mata ta duniya. Lokacin da malama Fatima ta yi hira da 'yan jarida shi ne ranar haihuwarta. Yayin da take sauraron kyakkyawan fata daga 'yan jarida, ta nuna fatan alheri ga dukkan mata musulmai na duniya, kana tana fatan dukkan mata musulmai za su ji dadin zaman duniya.

Kazalika ta bayyana cewa, a cikin wa'adinta na wakiliyar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa a wannan karo, tana son kara horar da lauyoyi mata a yankin kabilu na jihar Xinjiang, kana tana yin kokarin tabbatar da kare hakkin mata 'yan kananan kabilu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China