in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maria Mati, musulma 'yar kabilar Kirgiz ta dora muhimmanci kan aikin fama da talauci na yankin kabilar Kirgiz
2010-03-10 21:13:25 cri

Kabilar Kirgiz wata karamar kabila ce ta kasar Sin da ke bin addinin Musulunci, yankin kabilar Kirgiz na jihar Xinjiang ta kasar Sin kuma wani yanki ne da aka fi samun yawan 'yan kabilar a duk fadin kasar Sin. kasancewar yankin yana kan duwatsu da ke bakin iyakar kasar Sin, yanayin kasa a wurin ba kyau sam, don haka 'yan kabilar su kan yi fama da talauci mai tsanani. A matsayinta ta wakiliyar 'yan kabilar Kirgiz daya tak, Maria Mati, mataimakiyar shugaban ofishin kula da ayyukan fama da talauci na yankin kabilar Kirgiz ta dora muhimmanci sosai kan aikin fama da talauci na wurin. Kuma ta gaya wa wakiliyarmu cewa, bayan da aka samar da taimako ga yankin a 'yan shekarun da suka gabata, yankin ya samu babban ci gaba, kuma zaman rayuwar jama'a na wurin ya samu kyautatuwa kwarai. Ta ce,"Sakamakon kyautatuwar zaman rayuwar jama'a, yanzu 'yan kabilar Kirgiz sun canja ra'ayoyinsu da kuma fara koyon ilmin da ke iya taimaka musu wajen kara samun kudi. Yanzu yankinmu ya samu wata hanyar bunkasuwa, wato cin rani da raya sana'ar hamada da ta kiwon dabbobi kana da ta 'ya'yan itatuwa, muna fatan gwamnatinmu za ta iya kara kebe kudi gare mu domin kara yawan kudin da manoma za su samu."(Kande Gao)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China