Madam Mayinuer ta gabatar da cewa, sankarar cervical wani irin ciwo ne daya tak a duniya da aka san asalin cutar. Kuma kasar Amurka ta riga ta samu allurar rigakafin sankarar, kasashe fiye da 30 kuma sun riga sun fara amfani da wannan allura. Allurar na da tsada sosai, don haka Madam Mayinuer ta ba da shawarar shigar da wannan allurar a yankunan da aka fi samun yawan mata masu fama da sankarar kamar a jihar Xinjiang domin kyautata halin kiwon lafiya da matan wurin ke ciki. Kuma ta ce,"sankarar 'cervical' sankara ce ta biyu da mata mafi yawa ke fama da ita, don haka ana bukatar da shigar da allurar rigakafin sankarar cikin gaggawa. 'Yan mata na jihar Xinjiang su kan yi aure da wuri, don haka halin kamuwa da sankarar ya fi tsanani. Yanzu an riga an samu dabarar rigakafin sankarar, ya kamata a yi amfani da ita."(Kande Gao)