Mr. Wang ya ce, za a yi kokarin raya dandalin tattaunawar hadin gwiwar cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa da gina wani zaunannen dakin dandalin. Haka kuma, jihar Ningxia tana yin hadin gwiwa da Dubbai wajen kafa kwalejin Confucius. Sannan jihar tana kokarin kafa wata unguwa, inda ba za a rika buga haraji ba ga kayayyakin Musulmai domin raya masana'antun musulmai a jihar.
Mr. Wang ya kara da cewa, an riga an kafa unguwannin masana'antu biyu a jihar Ningxia, wato unguwar raya kayayyakin abinci na Musulunci da unguwar samar da kayayyaki ga musulmai domin jawo masu tafiyar da masana'antun samar da kayayyaki ga musulmai da su zo jihar Ningxia. (Sanusi Chen)