in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Han Yongdong, musulmi dan kabilar Sala ya ba da shawara kan gaggauta gida dakunan kwana a yankunan karkara
2010-03-08 20:34:06 cri

Kabilar Sala wata karamar kabila ce ta kasar Sin da ke bin addinin Musulunci. A matsayinsa na wakilin kabilar Sala daya tak, Han Yongdong, shugaban gundumar Xunhua ta kabilar Sala ta lardin Qinghai ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatin kasar Sin ta gaggauta gina dakunan kwana a yankunan karkara yayin da take daidaita tsarin tattalin arziki da kuma kara bukatun gida, domin sa kaimi ga raya birane da yankunan karkara gaba daya.

Han Yongdong ya kuma nuna cewa, ba kawai kara gaggauta gina dakunan kwana a yankunan karkara na iya ba da taimako wajen kara bukatun gida ba, har ma yana iya kyautata yanayin kwana na manoma, abin da ya fi muhimmanci kuma shi ne karfafa zukatan manoma wajen aikin samarwa. Kuma ya kara da cewa:"Muna fatan gwamnatin kasarmu za ta iya samar da kudin taimako wajen gina dakunan kwana, wato in mazauna yankunan karkara sun gina dakunan kwana, to gwamnatin za ta biya kudin taimako, lallai wannan aiki na da kyakkyawar makoma, ba kawai zai iya sa kaimi ga kasuwar kayayyakin gine-gine ba, har ma ya iya kyautata yanayin kwana na jama'a, ta haka za a iya sa kaimi ga raya sabbin yankunan karkara. Abu mafi muhimmanci shi ne wannan mataki zai iya samar da karfin gwiwa ga jama'a wajen aikin samarwa. Wato idan jama'a sun kashe kudinsu wajen kyautata dakunan kwana, to za su iya zuwa cin rani domin kara samun kudi. A hakika dai wannan wata madaidaiciyar hanya ce ga kasarmu wajen raya birane da yankunan karkara gaba daya."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China