in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma Hanlan, musulma 'yar kabilar Dongxiang na mai da hankali kan kafa makarantun kwana a yankunan karkara
2010-03-08 20:33:07 cri

Kabilar Dongxiang wata karamar kabila ce ta kasar Sin da ke bin addinin Musulunci. Sakamakon yanayi maras kyau, 'yan kabilar Dongxiang da ke gundumar Dongxiang ta lardin Gansu su kan zauna a wurare daban daban da ke kan duwatsu. Sabo da haka ko da yaushe yara 'yan kabilar ba su iya samun ilmi kamar yadda ya kamata ba. A matsayinta ta wakiliyar 'yan kabilar Dongxiang daya tak, Ma Hanlan ta dora muhimmanci sosai kan aikin samun ilmi. Ta gaya wa wakiliyarmu cewa, yayin da take yin bincike a yankunan karkara, wasu yara sun gaya mata cewa, a wasu lokuta sakamakon ruwan sama da kankara mai laushe, ba su iya zuwa makarantu ba, don haka suna fatan za su iya yin kwana a cikin makarantu. Sabo da haka Ma Hanlan ta tsai da kudurin bayar da wannan shawara a yayin taron NPC domin tallafa wa yara 'yan gundumar Dongxiang. Ta ce,"Mun riga mun yi gwajin kafa makarantun kwana 59 a garuruwa shida na gundumarmu, hakan ya kawo alheri ga yara 4000. Wannan aiki ya samu kyakkyawan sakamako sosai, kuma iyayen yara sun nuna maraba sosai ga makarantun kwana. Gundumar Dongxiang wata gunduma ce ta karamar kabila da ke fama da talauci sosai, don haka muna fatan gwamnatin kasarmu za ta iya ba mu tallafi wajen kafa makarantun kwana a dukkan garuruwan gundumarmu, ta yadda yara 'yan kabilar Dongxiang za su samu damar karatu kamar yadda yara na birane ke yi, ta haka kabilar Dongxiang za ta kara samun ci gaba."(Kande Gao)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China