in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma Xiaoqin, musulma 'yar kabilar Bao'an ta ba da shawara kan yin amfani da ruwan rawayan kogi don raya gundumar Jishishan
2010-03-05 16:55:09 cri

Kabilar Bao'an wata karamar kabila ce ta kasar Sin da ke bin addinin Musulunci, sakamakon yanayi maras kyau, ko ya yaushe 'yan kabilar Bao'an mazauna gundumar Jishishan ta lardin Gansu suna fama da karancin ruwa da kuma fama da talauci sosai. Sabo da haka, a matsayinta ta wakiliyar 'yan kabilar Bao'an daya tak, Ma Xiaoqin ta mai da hankali sosai kan bunkasuwar gundumarta. Kuma ta nuna cewa, in babu isasshen ruwa, to ba za a iya samun bunkasuwa ba. Don haka a yayin taron NPC, zan bayar da wata shawara kan raya wani babban aiki bisa tushen tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa domin amfani da ruwan rawayan kogi wajen raya gundumar Jishishan. Bayan da aka yi bincike, an kiyasta cewa, za a kashe Yuan miliyan 600 wajen gudanar da aikin. Amma bayan da aikin ya kammala, za a ba da kyakkyawan tasiri sosai ga gundumar Bao'an. Ta ce,"Wannan aiki ne mafi muhimmanci na gundumarmu wajen kyautata zaman rayuwar jama'a. Bayan da aka gudanar da aikin, za a iya warware matsalar karancin ruwa da ke gaban gonaki masu murabba'in kilomita kimamin dubu 67 da kuma mutane dubu 100, ta yadda za a taka rawa ga bunkasuwar kananan kabilu."(Kande Gao)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China