in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kasar Masar ya nuna yabo kan matakan da kasar Sin ta samar don inganta hadin gwiwar kasar Sin da ta kasashen Afirka
2009-11-11 17:26:34 cri
A ranar 8 ga watan Nuwamba, an bude wani taro na 4 na matsayin ministoci bisa tsarin dandalin tattaunawa game da hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a birnin Sham el-Sheik na kasar Masar, inda Mista Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin, ya yi bayani kan matakai 8 da gwamnatin kasar Sin ta samar don inganta hadin gwiwar da ake yi a tsakanin bangarorin Sin da Afirka. Sa'an nan, bayan bikin bude taron, wakilan rediyonmu sun yi hira da Mahmoud Mohieldin, ministan kasar Masar mai kula da aikin zuba jari, wanda ya nuna babban yabo kan matakan da kasar Sin ta samar, kamar yadda ya fadi cewa, 'A ganina, Mista Wen Jiabao ya yi hangen nesa wajen samar da matakan guda 8 domin ciyar da aikin hada kan kasashen Afirka da na kasar Sin gaba, wadanda a ganina, za su zama takamaiman matakai masu nagari da za su inganta huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Ta wadannan matakai, jama'ar kasashen Afirka za su kara samun damar yin karatu, da kuma shiga kwas na horo, sa'an nan za a kara samun 'yan Afirka da ke neman ilimi a kasar Sin, da kuma samun masana na kasar Sin da ke samar da gudunmawa a Afirka, inda suke ba da jagoranci wajen raya sana'ar noma da ta masana'antu, da kuma gina kayayyakin more jama'a. Shi ya sa matakan na da muhimmanci sosai ga raya kasashen Afirka, haka kuma sun samu karbuwa cikin jama'ar kasashen Afirka.'

Mahmoud Mohieldin yana ganin cewa, tallafin da kasar Sin ta samarwa kasashen Afirka ya shaida mana yadda gwamnatin kasar Sin take dora muhimmanci kan kyautata zaman rayuwar jama'ar kasashen Afirka, inda ya ce, 'Idan an dubi matakan tallafawa kasashen Afirka da kasar Sin ta samar a wajen taron koli na dandalin tattaunawar game da hadin kan kasashen Afirka da kasar Sin, wanda aka shirya a birnin Beijing a shekarar 2006, za a san cewa, kasar Sin tana mai da hankali kan zaman rayuwar jama'ar kasashen Afirka. Sa'an nan firmiyan Sin, Mista Wen Jiabao, ya kara sanya wasu sabbin abubuwa a cikin matakan da ka dauka a da, kamarsu samar da rancen raya kamfanonin kasashen Afirka wadanda ba su kai matsayin girma ba, da rage yawan kudin haraji ga kayayyakin kirar kasashen Afirka da ake sayar da su zuwa kasar Sin, da dai makamantasu. Irin wadannan matakai, ana ganin cewa, za su samar da wata ma'ana mai yakini ga bunkasuwar kasashen Afirka.'

Mista Mahmoud Mohieldin ya ce, tun da aka kafa dandalin tattaunawa na raya hadin kan kasar Sin da kasashen Afirka, ba kawai ba an zurfafa zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka, wanda ke da tarihi, har ma an samar da wani dandalin, inda ake cinikayya da hadin gwiwa, da kuma kawo wa kasashen Afirka takamaimiyar moriya. Kamar yadda ya fadi cewa, 'dandalin tattaunawa na inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya riga ya zama wani tsari mai muhimmanci. Kamar yadda muka ganewa idanunmu, mun gamu da rikicin hada-hadar kudi, da karancin abinci da na makamashi, wadanda sun sa kasashen duniya suka ji radadi cikin shekaru 3 da suka gabata. Amma, duk da haka, yawan cinikin da aka yi a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya karu da kashi 33% a ko wace shekara. Shi ya sa nake ganin cewa, sabbin matakan da Mista Wen Jiabao ya sanar mana, za su sa kasar Sin da kasashen Afirka su kara yin hadin gwiwa, ta yadda za su kara taka muhimmiyar rawa a duniya.'(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China