logo

HAUSA

Zhao Lijian: Gwamnatin Amurka ta yi watsi da aikin kare rayukan al’ummun ta da ma na sauran al’ummun duniya

2021-12-23 20:54:36 CRI

Zhao Lijian: Gwamnatin Amurka ta yi watsi da aikin kare rayukan al’ummun ta da ma na sauran al’ummun duniya_fororder_u=2334474333,4189136511&fm=15&fmt=auto

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana Amurka a matsayin babbar kasa mai karfin ci gaba, ta fuskar kiwon lafiya da albarkatu masu nasaba da hakan, wadda ta gaza wajen kare rayukan al’ummun ta daga annobar COVID-19.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a Alhamis din nan, ya ce ya zuwa ranar Laraba 22 ga watan Disamban nan, adadin wadanda suka rasu sakamakon harbuwa da COVID-19 a Amurka ya kai mutum sama da 810,000, adadin da ya kai kaso 15 bisa dari na jimillar wadanda cutar ta hallaka a duniya, kana jimillar wadanda suka harbu da ita a kasar kadai, ta kai mutum sama da miliyan 51, adadin da ya kai kaso 19 bisa dari na daukacin wadanda cutar ta harba a duniya baki daya.

Jami’in ya kara da cewa, tsohuwar gwamnatin Amurka da ta gabata, da gangan, ta rika mayar da annobar abun wasa, ta rika fitar da bayanai masu kautar da hankulan al’umma daga gaskiya, wanda da haka ta barnata dama mai kyau ta kandagarki da shawo kan annobar. Kari kan hakan, Amurka ta shafe lokaci tana zargin wasu sassa, tare da kitsa karairayi marasa ma’ana, da siyasantar da batun annobar, wanda hakan ya haifarwa kasar gibi, tare da yin karen-tsaye ga hadin gwiwar ta da sauran sassan duniya, a fannin aiwatar da matakan yaki da cutar ta COVID-19.

Kari kan hakan, Zhao ya ce yayin da ake fama da wannan annoba, Amurka ta kakaba takunkumi kan Iran, da Cuba, da Venezuela da Syria, wanda hakan ya sanya kasashen cikin yanayi mai tsanani, ta fuskar karbar tallafin jin kai a kan lokaci, wanda hakan ya haifar da tafiyar hawainiya wajen yaki da annobar.  (Saminu)

Saminu