logo

HAUSA

Algeria ta samu rahoton farko na nau’in Omicron

2021-12-15 11:05:31 CMG

Algeria ta samu rahoton farko na nau’in Omicron_fororder_211215-A3-Aljeriya

Hukumomin lafiyar kasar Algeria sun sanar a ranar Talata cewa, an tabbatar da rahoton farko na cutar COVID-19 nau’in Omicron a kasar, kafafen yada labaran kasar sun bada rahoton.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito cewa, wani dan kasar waje da ya shiga kasar Algeria a ranar 10 ga watan Disamba ne ke dauke da cutar bayan gwajin da aka yi masa a yayin da ya isa filin jirgin saman kasa da kasa na Algiers. Samakon gwajin da aka yiwa mutumin, wanda cibiyar Institut Pasteur d'Alger ta kasar ta gudanar, an tabbatar a ranar Talata cewa mutumin na dauke da cutar COVID-19 nau’in Omicron.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, an gano nau’in Omicron na farko ne a kasar Afrika ta Kudu, ya zuwa yanzu, an samu yaduwar nau’in cutar a kasashen duniya kusan 65.

Hukumomin lafiyar kasar Algeria sun bayyana a ranar Talata cewa, an samu sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 kimanin 280, da kuma sabbin mutanen da suka mutu hudu a cikin sa’oi 24 da suka gabata, inda jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai 213,288, sannan cutar ta kashe mutane 6,155 a kasar.(Ahmad)

Ahmad