logo

HAUSA

Karuwar masu kamuwa da COVID-19 ya tilasta maida darasi ta intanet da kuma daukar sabbin matakai a Amurka

2021-12-17 10:41:40 CMG

Karuwar masu kamuwa da COVID-19 ya tilasta maida darasi ta intanet da kuma daukar sabbin matakai a Amurka_fororder_211217-Ahmad2

Yayin da adadin mutanen da ake kwantarwa a asibiti sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 ke karuwa, da kuma yawaitar mutanen da cutar ke kashewa a duk fadin kasar Amurka gabanin hutun karshen shekara, lamarin ya tilasta wasu jami’o’in kasar mayar da tsarin koyarwarsu ta intanet, da kuma ba da sabon umarnin amfani da takunkumin rufe fuska da yin riga-kafin cutar.

Alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta CDC ta fitar ya nuna cewa, ana samun sabbin masu kamuwa da cutar kusan 118,000 a kullum, yayin da aka samu rahoto mafi yawa da ya kai kusan 200,000 da suka kamu da cutar a duk fadin kasar Amurka a ranar Litinin.

Yawan mutanen da ake kwantarwa a asibiti sakamakon kamuwa da COVID-19 a kasar ya karu da kashi 46 bisa 100 idan an kwatanta da wata guda ta ya gabata, kamar yadda alkaluman hukumar lafiya da yiwa al’umma hidima ta kasar Amurka suka bayyana.

Kwararrun masana kiwon lafiya sun ce, karuwar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 ya faru ne sakamakon yaduwar sabbin nau’ikan cutar na Delta da Omicron wadanda ke yaduwa cikin sauri a duk fadin kasar ta Amurka.

Nau’in Omicron, wanda ake tsammanin yafi nau’in Delta hadari, an samu yaduwarsa a jahohin Amurka a kalla 38 ya zuwa ranar Alhamis, tun bayan samun rahoton farko na bullar nau’in cutar a jahar California a ranar 1 ga watan Disamba.(Ahmad)

Ahmad