logo

HAUSA

MDD ya yaba da yadda aka rantsar da ‘yan majalisun dokokin Sudan ta Kudu

2021-08-05 10:56:32 CRI

MDD ya yaba da yadda aka rantsar da ‘yan majalisun dokokin Sudan ta Kudu_fororder_a1ec08fa513d269759eef3ab1eb7a5fb43166c2272ba

Tawagar MDD dake Sudan ta Kudu, ta yi maraba da yadda aka rantsar da ‘yan majalisun dokokin kasar 504, da kuma mambobin majalisar zartaswar kasar 84, abin da ke zama wani babban ci gaba da aka samu a shirin wanzar da zaman lafiyar kasar.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Juba, fadar mulkin kasar, wakilin musamman na babban sakataren MDD a Sudan ta Kudun, Nicholas Haysom ya bayyana fatan cewa, sabbin ‘yan majalisun, za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Haysom ya ce, “Muna da tabbacin cewa, ‘yan majalisun za su kara kaimi wajen sauke nauyin dake wuyansu, duba da cewa, har yanzu ba a kai ga cimma burin da ake fata kamar yadda yake cikin yarjejeniyar ba.

Ya bayyana cewa, nada Madam Jemma Nunu Kumba, mace ta farko a matsayin kakakin majalisar dokokin kasar, wata babbar nasara ce, daga cikin burin da ake fatan cimmawa a cikin yarjejeniyar zaman lafiyar kasar, na baiwa mata kaso 35 cikin 100 a tsarin shugabancin kasar.

Haysom ya ci gaba da cewa, abin farin ciki ne ganin yadda aka rantsar da sabbin ‘yan majalisun, muna kuma fatan ganin, sun fara aiki gadan-gadan a ‘yan kwanaki dake tafe.(Ibrahim)

Ibrahim