Sakatare Janar na MDD ya tattauna da Firaministan Habasha dangane da yanayin jin kai a yankin Tigray
2021-07-10 16:40:40 CMG
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya tattauna da Firaministan Habasha Abiy Ahmed, kan tsanatar yanayin jin kai a yankin Tigray na kasar.
Wata sanarwa da Stephane Dujjaric, kakakin sakatare janar din fitar, ta ce Antonio Guterres ya yi maraba da tabbacin da firaministan ya bayar cewa, gwamnatinsa za ta bada damar shiga yankin Tigray ga kungigoyin agaji, tare da alkawarin cewa, za a mayar da hidimomin bukatun rayuwa kamar wutar lantarki da tsarin sadarwa cikin gaggawa a yankin.
Sakatare Janar din ya kuma yabawa alkawarin gwamnatin Habasha na amfani da tsagaita bude wuta a yankin, wajen saukaka kai daukin gaggawa, ciki har da ba jiragen saman MDD damar zirga-zirga a yankin da kuma taimakawa ayyukan gona.
Antonio Guterres ya jaddada kira ga dukkan bangarorin kasar, sun sauke nauyin dake wuyansu na kare fararen hula da samar da agajin jin kai ba tare da tsaiko ba, da kuma kiyaye dokokin jin kai na duniya. (Fa’iza Mustapha)