Wakilin kasar Sin ya yi kira da a yi kokarin warware takaddamar siyasa a DRC
2021-07-08 10:57:05 CRI
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira da a kara kaimi, wajen ganin an daidaita takaddamar siyasar da ake fama da ita a Jamhuriyar demokiradiyar Congo(DRC) da kuma inganta yanayin tsaron kasar dake gabashin Afirka.
Dai Bing ya bayyana haka ne, ga zaman kwamitin sulhun MDD, yana mai cewa, an samu ingantuwar yanayin siyasar kasar a halin yanzu. Ya bayyana cewa, yadda aka kafa sabuwar gwamnati, aka kuma fara amfani da wani shirin raya kasa na shekaru 3, ya nuna kudirin Shugaba Felix Tshisekedi, da gwamnatin kasar na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da aiwatar da gyare-gyare, da inganta zamantakewar al’umma, da kara karfin shugabanci. A don haka, kasar Sin tana fatan dukkan bangarori na kasar, za su hada kansu a matsayin tsintsiya madaurin ki daya, su kuma aiki tare, don cimma wadannan manufofi.
Ya bayyana cewa, yanayin tsaron da ake ciki a kasar, ya kasance abin damuwa, ganin yadda ake kara samun tashin hankali na masu dauke da makami. Ya kuma shaidawa kwamitin sulhun cewa, ana fatan gwamnatin DRC, za ta yi kokarin ganin an kwance damarar Makai, da kawo karshen kungiyoyin ‘yan tawaye, a kuma dama da al’ummu, a aiwatar da shirin daidaita al’amura, a kuma magance rikici da tashin hankali daga tushe yadda ya kamata.(Ibrahim)