Zhao Lijian: Sama da kasashe 90 sun bayyana adawa da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin
2021-07-20 19:34:23 CRI
An kammala zama na 47, na hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD. Kafin hakan kasashe sama da 90 sun nuna goyon bayan su ga adalci, inda suka nuna cikakkiyar adawar su da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda wasu sassan yammacin duniya ke yi da sunan kare hakkin bil Adama.
Da yaka tabbatar da hakan yayin taron manema labarai na Talatar nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce hakan ya ma wuce goyon baya ga kasar Sin kadai, domin kuwa ya shaida yadda kasashen duniya ke mara baya ga manufofi da ka’idojin cudanya na MDD, da kuma gaskiya da adalci a matakin kasa da kasa. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba
- Sakatare Janar na MDD ya tattauna da Firaministan Habasha dangane da yanayin jin kai a yankin Tigray
- Wakilin kasar Sin ya yi kira da a yi kokarin warware takaddamar siyasa a DRC
- UNICEF na neman kudi tallafawa yara miliyan 4.5 a kasar Sudan ta Kudu
- Jami’in MDD ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yankin Tigray