logo

HAUSA

AU ta bukaci a kaucewa duk wani nau’in rikici a Tunisia

2021-07-28 10:40:14 CRI

Shugaban hukumar kungiyar tarayyar Afirka wato AU a takaice Moussa Faki Mahamat, ya bukaci a bijirewa duk wani nau’i na rikici a kasar Tunisia, yana mai kira da a hau teburin sulhu domin warware matsalolin kasar da ke arewacin nahiyar Afirka.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Tunisia jiya Talata 27 ga wata, inda ya ce yana bibiyar yanayin da siyasar kasar ke ciki a baya bayan nan.

A ranar Lahadi 25 ga wata ne zanga-zanga ta barke a larduna da dama na kasar ta Tunisia, inda masu zanga-zangar suka bayyana fushinsu game da tabarbarewar tsarukan kiwon lafiya da na tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa, suna masu kira da sauyin gwamnati da rushe majalisar dokokin kasar dake karkashin shugabancin Rached Ghannouchi, shugaban jam’iyyar Ennahdha.

Moussa Faki Mahamat, ya kuma bayana kudurin AU na girmama kundin tsarin mulkin kasar Tunisia, da wajibcin tabbatar da zaman lafiya da bijirewa duk wani rikici da kuma inganta hawa teburin sulhu domin shawo kan matsalolin dake akwai a kasar. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha