logo

HAUSA

MINUSMA ta bukaci a sako shugaban rikon kwaryar Mali da firaminista

2021-05-25 11:21:03 CRI

Rundunar hadin gwiwar bangarori daban daban ta MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a Mali (MINUSMA), a jiya Litinin ta wallafa wata sanarwa a shafinta na twita inda ta bukaci a sako shugaban rikon kwaryar kasar Mali, Bah N'Daw, da firaministan kasar Moctar Ouane.

MINUSMA ta kara da cewa, tilas ne a tabbatar da lafiyar shugabannin da ake tsare da su. Kuma tana ci gaba da tattaunawa da kungiyoyin ECOWAS da tarayyar Afrika AU, karkashin wani kwamitin sanya ido kan mika mulki na kasar, da sauran bangarori masu ruwa da tsaki na kasa da kasa dake taimakawa shirin mika mulkin kasar.(Ahmad)

Ahmad