logo

HAUSA

AU ta yi kira ga Somalia da Kenya sun tattauna domin warware rikicin kan iyaka

2021-01-27 10:32:15 CRI

Tarayyar Afrika AU, ta yi kira ga kasashen Somalia da Kenya, sun hau teburin sulhu domin warware rikicin kan iyaka, wanda ya kai ga mutuwar mutane 11 da jikkatar wasu da dama a ranar Litinin.

Shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat, ya kuma yi kira ga kasashen biyu makwabta, su dakatar da bude wuta tare da rungumar tattaunawa karkashin jagorancin kungiyar raya gabashin Afrika IGAD, domin warware sabanin dake tsakaninsu.

Furucin na Moussa Mahamat na zuwa ne, bayan gwamnatin Somalia ta ce an kashe mutane 11 yayin da wasu da dama suka jikkata, biyo bayan fadan da aka gwabza a garin Beled Hawo, tsakanin dakarun kasar da mayakan yankin Jubbaland mai cin gashin kai.

Dukkan bangarorin biyu dai, sun yi ikirarin samun nasara, amma wasu majiyoyi masu zaman kansu a garin sun bayyana cewa, an ci gaba da fada a yinin ranar, lamarin da ya daidaita garin. (Fa’iza Mustapha)

Faeza