logo

HAUSA

Kamaru ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa hukumar kula da magunguna ta Afrika

2021-07-12 13:01:48 CRI

Kamaru ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa hukumar kula da magunguna ta Afrika_fororder_非洲药品

Gidan talabijin din kasar Kamaru na CRTV ya bada rahoton a ranar Lahadi, cewar shugaban kasar Paul Biya, ya sanya hannu kan yarjejeniyar kafa hukumar lura da magunguna ta Afrika (AMA), a matsayin wata hukuma ta kungiyar tarayyar Afrika AU.

An amince da yarjejeniyar kafa AMA ne a watan Fabrairun 2019. A makon jiya, majalisar dattijan kasar Kamaru ta amince da kudurin doka wadda ta sahhalewa shugaban kasar ya rattaba hannu kan yarjejeniyar.

AMA za ta kasance a matsayin wata hukuma ta nahiya, wacce za ta dinga lura da dokokin dake shafar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a nahiyar Afrika. Za ta samar da tsarin dokokin dake shafar kyawun magunguna, da ingancinsu, da kuma tabbatar da nagartar magungunan da yadda za a samar da muhimman magunguna masu rahusa da fasahohin kiwon lafiya ga nahiyar.(Ahmad)