logo

HAUSA

Shugaban Zambia Ya Kaddamar Da Tashar Lantarki Da Sin Ta Gina A Kasar

2021-07-24 15:53:20 CRI

Shugaban Zambia Ya Kaddamar Da Tashar Lantarki Da Sin Ta Gina A Kasar_fororder_微信图片_20210724155254

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya kaddamar da wata tashar lantarki da Sin ta gina a gundumar Chikankata na kudancin kasar, yana mai cewa tashar ta nuna jajircewa da juriyar gwamnati na tabbatar da biyan bukatun lantarki na kasar.

Kamfanin SinoHydro na kasar Sin ne ya aiwatar da aikin ginin tashar ta Kafue Gorge Lower da ake sa ran za ta samar da karin megawatt 750 ga turakun lantarki na kasar.

A cewar shugaban, ba wadatar makamashi kadai tashar za ta samar ga kasar ba, har ma ta zama wata cibiyar samar da lantarki a yankin kudancin Afrika.

Ya kuma godewa kasar Sin bisa gudunmuwarta ta ciyar da kasar gaba, yana mai cewa Sin ta kasance aminiya ta kwarai ga Zambia.

A nasa bangaren, jakadan Sin a Zambia Li Jie, ya ce tashar lantarkin wani muhimmin aiki ne karkashin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, da kuma shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”.

Ya kara da cewa, aikin zai ba da gudunmuwa ga kokarin Zambia na shawo kan karancin lantarki da bunkasa ci gaba a fannonin tattalin arziki daban-daban. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha