logo

HAUSA

Kasar Sin ta mika ta’aziya game da mutuwar tsohon shugaban Zambia

2021-06-18 21:01:44 CRI

Kasar ta mika ta’aziya game da mutuwar tsohon shugaban Zambia_fororder_1

Kasar Sin ta isar da ta’aziyarta game da mutuwar tsohon shugaban kasar Zambia Mr. Kenneth Kaunda.

Da yake bayyana haka Jumma’ar nan, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, mai magana yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, marigayi Mr Kaunda shi ne ya kafa alaka tsakanin Sin da Zambia. Ya kuma ciyar da kalmar kyakkyawar abokantaka gaba da kafa cikakkiyar alaka tsakanin Sin da Zambia a bayyane. (Ibrahim)