logo

HAUSA

An yi jana’izar shugaban kasar Zambia na farko

2021-07-08 10:56:11 CRI

An yi jana’izar shugaban kasar Zambia na farko_fororder_赞比亚

Jiya ne aka yi jana’izar shugaban kasar Zambia na farko, marigayi Kenneth Kaunda, bayan kammala zaman makoki na kwanaki 21, inda shugaban kasar Edgar Lungu ya ayyana ranar 28 ga watan Afrilu, ranar haihuwar marigayin a matsayin ranar hutu a fadin kasar.

An binne gawar marigayi Kaunda, wanda ya mulki kasar daga shekarar 1964 zuwa 1991 ne, a wurin shakatawa na Embassy Park dake Lusaka, babban birnin kasar, wurin da aka kebe don bisine tsoffin shugabannin kasar. Bayan kammala bikin bisine gawar ce kuma, aka shiga addu’o’i a majami’ar Cathedral ta Holy Cross.

Shugaba Lungu da Hakainde Hichilema, babban mai kalubalantarsa a manyan zabukan kasar dake tafe, na daga cikin wadanda suka halarci addu’o’in, baya ga wasu manyan mutane, da suka hada da tsohon shugaban kasar Mozambique Joaqium Chissano, da tsohon shugaban kasar ta Zambia Rupiah Banda.

An dai gudanar da addu’o’i a majami’ar ce, karkashin tsauraran matakan yaki da annobar COVID-19, an kuma watsi bikin kai tsaye ta kafar talabijin din kasar, tare da nuna yanayi na alhini, inda jama’a suka sanya bakaken kaya, wasu kuma na rike da mayanin goge fuska, alamar tsohon shugaban kasar ta nuna zaman lafiya. Addu’ar da aka gudanar a majami’ar, ita ce ta karshe da aka gudanar a dukkan garuruwa dake larduna 10 na kasar, inda aka zagaye da gawar, a wani mataki na zaman makokin da aka ayyana a fadin kasar. Marigayi Kaunda dai ya rasu ne, a ranar 17 ga watan Yuni, yana da shekaru 97 a duniya. (Ibrahim)