logo

HAUSA

An fara samun raguwar masu kamuwa da COVID-19 a Zambia

2021-07-05 11:07:36 CRI

An fara samun raguwar masu kamuwa da COVID-19 a Zambia_fororder_疫苗

Ma’aikatar lafiya ta kasar Zambia ta bayyana cewa, an fara samun gagarumar raguwar yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar a cikin makon da ya gabata, idan aka kwatanta da makonnin baya.

Da yake karin haske kan lamarin, babban sakatare a ma’aikatar lafiyar kasar mai kula da manyan ayyuka, Kennedy Malama, ya bayyana cewa, alkaluman da aka tattara a makonnin biyun da suka gabata, sun nuna raguwar yawan sabbin masu kamuwa da cutar, daga mutum 19,535 zuwa mutum 15,714. Haka kuma baki dayan yawan masu kamuwa da cutar a mako, ya dan ragu daga kaso 26 cikin 100 zuwa kaso 24 cikin 100.

Ya kara da cewa, an dan samu raguwar yawan wadanda ake kwantarwa a asibiti sanadiyar cutar da yawan mamata, yana mai cewa, ma’aikatar ta himmatu wajen tabbatar da dorewar hakan. Sai dai ya jaddada bukatar magance tushen annobar, ta hanyar yakarta daga cikin al’umma.

Ya kuma sanar da cewa, a yau ne kasar za ta karbi karin alluran riga kafin kamfanin AstraZeneca 228,000. Ya kuma godewa shirin nan na COVAX, bisa ga goyon bayan da ya baiwa kasarsa, wajen samu kashin farko na riga kafin,don shirin yi wa ‘yan kasar alluran riga kafin.(Ibrahim)