logo

HAUSA

Masar ta yi watsi da sanarwar firaministan Habasha game da ginin sabbin madatsun ruwa

2021-06-01 12:40:14 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar, ta yi tir da wata sanarwa da firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana shirin kasar sa na gina sabbin kanana da matsakaitan madatsun ruwa sama da 100 a Habasha, yayin aiwatar da kasafin kudin kasar mai zuwa.

Sanarar da ma’aikatar wajen Masar ta fitar game da wannan batu, ta ce kalaman firaminista Ahmed na nuna aniyar Habasha ta yin yadda ta ga dama, game da yadda take mu’amala da kogin Nilu, da sauran sassan ruwayen kasa da kasa da take cin gajiyar su tare da kasashe makwaftan ta.

Masar dai na cewa, kasashe masu kusanci da kogin Nilu na da hakkin cin gajiya daga albarkatun sa. Sai dai kuma wadannan irin ayyuka da Habasha ke burin aiwatarwa, ya dace su biyo bayan cikakken tsarin tuntuba, da cimma matsaya tare da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, musamman ma kasashen da ke amfana kai tsaye daga albarkatun ruwan kogin na Nilu.  (Saminu)

Saminu