logo

HAUSA

Ayyukan agaji na ci gaba da gudana a yankin Tigray na Habasha duk da yanayin tsaro

2021-05-06 13:35:10 cri

Ofishin kula da agajin jin kai na MDD, ya ce yanayin tsaro mara tabbas a yankin Tigray na Habasha, na barazana ga ci gaba da gudanar da ayyukan bada agajin da aka tsara zai kai ga dukkan mabukata.

Ofishin ya kara da cewa, har yanzu, rabon abinci shi ne muhimmin bangaren aikin agajin. Yana mai cewa, zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, gwamnati da shirin samar da abinci na duniya (WFP), sun raba sama da metric ton 19,000 na abinci ga mutane miliyan 1.1 a larduna 35 na yankin Tigray. (Fa’iza Mustapha)