logo

HAUSA

An sanya sabuwar ranar gudanar da babban zaben kasar Habasha

2021-05-21 10:36:50 CRI

An sanya sabuwar ranar gudanar da babban zaben kasar Habasha_fororder_微信图片_20210521143338

Hukumar zabe ta kasar Habasha (NEBE), ta sanar da ayyana ranar 21 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar da za a gudanar da babban zaben kasar.

Kakakin hukumar NEBE Solyana Shimelis, ya ce an tsara sabon jadawalin zaben ne bayan la’akari da bukatar kammalawa da sufurin takardun zabe zuwa mazabun dake fadin kasar.

A baya, an sanya 5 ga watan Yuni a matsayin ranar babban zaben karo na 6, amma na wucin gadi.

A cewar kakakin, baya ga zabukan ‘yan majalisun dokoki da na jihohi, za a gudanar da zaben raba gardama kan yuwuwar kirkirar sabuwar jiha ta 11 a ranar 21 ga watan na Yuni.

Fiye da al’ummar Habasha miliyan 31.7, ciki har da sama da mutane miliyan 1.2 masu kada kuri’a a Addis Ababa babban birnin kasar ne suka yi rejista domin kada kuri’a a babban zaben karo na 6 dake tafe. (Fa’iza Mustapha)