logo

HAUSA

Shugaban Masar da jagoran AU sun tattauna batun dam din Habasha

2021-05-09 16:48:42 CRI

Shugaban Masar da jagoran AU sun tattauna batun dam din Habasha_fororder_微信图片_20210509212254

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, a ranar Asabar ya tattauna da  shugaban kasar jamhuriyar demokuradiyyar Kongo DRC, Felix Tshisekedi, kana shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afrika na yanzu, game da cigaban da aka samu kan batun aikin gina madatsar ruwan Habasha ta (GERD) a kogin Nile.

Kasar Masar tare da Sudan da suke makwabtaka da kogin, sun sha bayyana damuwa game da mataki na kashin kai da Habasha ta dauka na aikin cike madatsar ruwan GERD a zagaye na biyu a wannan shekara, kamar yadda ta yi a shekarar bara, ba tare da cimma matsaya ba a tsakanin kasashen uku da batun ya shafa kan yadda za a gudanar da aikin gina dam din.

Masar da Sudan suna son a warware batun karkashin tsarin bangarorin kasa da kasa hudu da suka hada da kungiyar tarayyar Afrika AU, da Amurka, da kungiyar tarayyar Turai, da kuma MDD, domin a samu damar cimma yarjejeniya da ake fata, sai dai wannan bukata bata samu amincewar bangaren Habasha ba.

Shugaban Masar ya bayyana a lokacin tattaunawarsa da Tshisekedi cewa, kasar Masar ba zata laminci lalata mata hanyar samun ruwan shanta ba, kuma tilas ne a cimma matsaya bisa yarjejeniyar da doka ta tanada wacce ta baiwa Masar din ‘yancin samun ruwan sha wacce kuma zata kwantar da hankula da tabbatar da kiyaye zaman lafiyar shiyyar.

A nasa bangaren, shugaban na Kongo DRC ya jaddada aniyarsa na yin aiki tukuru game da wannan muhimmin batu domin cimma nasarar daidaita bangarorin uku da lamarin ya shafa.

Tshisekedi ya yabawa kokarin da Masar ke yi wajen tabbatar da cimma matsaya bisa adalci domin biyan muradun kasashen uku.

Kasar Habasha ta fara aikin gina madatsar ruwan GERD a shekarar 2011. Masar ta nuna damuwa cewa aikin zai iya shafar ruwan da take amfani  da shi a duk shekara da ya kai cubik mita biliyan 55.5 wanda take samu daga kogin na Nile, yayin da Sudan ma ta gabatar da makamancin wannan korafi game da wannan aikin na sama da dala biliyan hudu.(Ahmad)