logo

HAUSA

Hatsarin jirgin sama ya yi sanadin mutuwar babban hafsa sojin Nijeriya tare da wasu jami’ai 10

2021-05-22 16:30:58 CRI

Rundunar sojin tarayyar Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar jami’anta 11, ciki har da babban hafsan sojin kasar Ibrahim Attahiru, bayan da jirgin saman da suke ciki ya yi hatsari da yammacin jiya Jumma’a ranar 21 ga wata a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin kasa Mohammed Yerima ya fitar, ta bayyana cewa, Ibrahim Attahiru tare da sauran jami’an 10, suna kan hanyarsu ce ta zuwa garin Kaduna daga birnin Abuja, hedkwatar kasar, a lokacin da jirgin ya yi hatsari a kusa da filin jirgin saman kasa da kasa na Kaduna.

Cikin wata sanarwa ta daban, kakakin rundunar sojin saman kasar Edward Gabkwet, ya yi nuni da cewa, har yanzu ba a kai ga gano musabbabin hatsarin ba tukuna.

A nasa bangaren, shugaban kasar tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana kaduwa da aukuwar hatsarin, yana mai cewa, lamarin ya jefa shi cikin jimami.

Cikin wata sanarwa a jiya, shugaba Buhari ya ce, hatsarin babban gibi ne ga kasar, a daidai lokacin da dakaru suka dukufa wajen kawo karshen kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta. Yana mai bayyana jami’an da suka mutu a matsayin gwarazan da suka sadaukar da ransu ga tsaro da zaman lafiyan kasar. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha