logo

HAUSA

Sojojin Nijeriya sun cafke wasu mutane 13 da ake zargin mayakan BH ne

2021-05-10 10:35:31 CRI

Sojojin Nijeriya sun cafke wasu mutane 13 da ake zargin mayakan BH ne_fororder_BH

Rundunar sojin Nijeriya ta cafke wasu mutane 13 da ake zargin mayakan BH ne, a jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Mohammed Yerima, ya ce an cafke mutanen ne a yankin Filin Lazio na unguwar Hotoro a Kano, biyo bayan wani samame.

Ya ce ana kai samamen ne da nufin cafke mayakan dake neman buya a duk wani yanki na jihar ta Kano. (Fa’iza Mustapha)

Faeza