logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun kashe mutane 323 tare da sace 949 cikin watanni 3 a jihar Kadunan Nijeriya

2021-05-01 15:44:27 CRI

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta tabbatar da cewa, jimilar mutane 323 aka kashe tare da sace 949, yayin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai jihar cikin watanni 3 da suka gabata.

Rahoton da gwamnatin ta fitar dangane da yanayin tsaro cikin rubu’in farko na bana, ya kuma tabbatar da cewa, sojoji sun halaka ‘yan bindiga 64 tare da cafke wasu da dama a tsakanin wancan lokaci.

Kwamishinan kula da tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya ce rahoton ya kunshi hare-hare daban-daban da suka auku a jihar, wadanda suka hada da fashi da makami da na ramuwar gayya da sace-sacen mutane da satar shanu.

Ya kara da cewa, daga cikin mutanen da suka mutu sanadiyyar wadancan hare-hare, akwai mata 20 da yara 11.

Bugu da kari, ya ce an kashe ‘yan bindiga da dama yayin wasu hare-hare ta sama kimanin 150 da rundunar sojin saman kasar ta gudanar cikin watannin 3 na farkon bana. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha