logo

HAUSA

Rikice-rikice na kawo tarnaki ga ayyukan jin kai a jihar Borno

2021-04-17 15:37:39 CRI

Rikice-rikice na kawo tarnaki ga ayyukan jin kai a jihar Borno_fororder_borno

MDD ta ce rikice-rikice tsakanin kungiyoyin ‘yan ta’adda da sojojin gwamnati a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, na yi wa ayyukan jin kai a jihar tarnaki.

Stephane Dujarric, kakakin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ma’aikatan jin kai na MDD na ci gaba da samun rahotanni masu tayar da hankali dangane da arangamar da ake tsakanin ‘yan ta’adda da sojojin kasar a garin Damasak na jihar. Ko a baya-bayan nan, wasu ‘yan ta’adda sun bi gida-gida suna neman fararen hula ma’aikatan jin kai.

Ya kara da cewa, a makon da ya gabata ma, an kai hari kan kadarorin ma’aikatan jin kai a Damasak, inda aka lalata ofisoshin kungiyoyin ayyukan jin kai a kalla 5, da tarin motocinsu, da wajen adana kayayyaki na tafi da gidanka, da tankunan ruwa, da wata cibiyar kula da lafiya, da ta kula da masu fama da tamowa. An kuma samu karin rahotannin rikice-rikice a wannan makon.

Stephane Dujarric, ya yi gargadin cewa, wadannan hare-hare za su yi tasiri kan ayyukan jin kai da kariyar da ake ba kusan ‘yan gudun hijira 9,000 da wasu mutane 76,000 na yankin dake ba ‘yan gudun hijirar mafaka. (Fa’iza Mustapha)

Faeza