logo

HAUSA

Nijeriya ta yi alkawarin karfafa goyon baya ga ayyukan raya yankin tafkin Chadi

2021-04-14 10:07:26 CRI

Nijeriya ta yi alkawarin karfafa goyon baya ga ayyukan raya yankin tafkin Chadi_fororder_src=http___dingyue.ws.126.net_u7L6NxOUdrIcnoJMvMODwQbPkvMfP1g9KmK7A6lEbh6Hb1543035174068compressflag.jpeg&refer=http___dingyue.ws.126

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa, za ta taimaka wajen karfafa rayawa da farfado da yankin tafkin Chadi.

Ministar kula da ayyukan jin kai ta kasar, Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar, bayan wani taron ministoci da Bankin Duniya ya kira jiya ta kafar bidiyo, game da yankin na tafkin Chadi, inda ta ce kasarta za ta mayar da hankali kan ayyukan raya yankin.

Ministar ta ce kasar za ta mayar da hankali kan dandamalin hadin kai na cikin gida da na yanki domin karfafa tattaunawa da tattara bayanai da kuma yada su a yankin.

A cewarta, yankin na fuskantar tarin kalubalen dake kara masa rauni, tana mai cewa kungiyar BH na ayyukanta a kasa da kasa, inda ta ke fadada munanan ayyukanta daga Nijeriya zuwa Kamaru zuwa Chadi da Niger. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha