logo

HAUSA

An saki mutane 53 da aka sace a Nijeriya

2021-02-23 09:50:23 CRI

Gwamnan jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Nijeriya, Abubakar Sani Bello, ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin kubutar da dukkan fasinjoji 53 da ‘yan bindiga suka sace a kauyen Kundu na jihar a ranar 14 ga watan Fabreru.

Lamarin ya auku ne kwanaki 3 gabanin sace dalibai da malamansu da aka yi, a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake garin Kagara na jihar ta Neja.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Minna, Gwamnan Abubakar Bello, ya ce an saki fasinjojin ne bayan an yi ta jerin tuntuba da tattaunawa, da kuma aiki tukuru.

Ya kara da cewa, har yanzu ana ci gaba da kokarin ceto daliban kwaleji, da wasu gungun ‘yan bindiga suka sace biyo bayan harin da suka kai makarantarsu a ranar Larabar da ta gabata. (Fa’iza Mustapha)

Bello