logo

HAUSA

Sin ta biya dukkan kason gudunmuwarta ga kasafin kudin MDD na 2021

2021-04-14 10:33:40 CRI

Sin ta biya dukkan kason gudunmuwarta ga kasafin kudin MDD na 2021_fororder_中国与联合国

Kasar Sin ta biya dukkan kason gudunmuwarta ga kasafin kudin MDD da na kotun manyan laifuffukan kasa da kasa na majalisar, na shekarar 2021.

A cewar kungiyar wakilan kasar Sin a majalisar, kafin sannan, tuni Kasar ta riga ta biya dukkan kudaden da suka rage na ayyukan wanzar da zaman lafiya tsakanin shekarar 2020/2021. Kana ta biya gudunmuwar da take bayarwa kowacce shekara da dukkan sauran kudade.

Ya kara da cewa, Kasar Sin za ta ci gaba da sauke nauyin dake wuyanta da aiki da dukkanin bangarori domin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil Adama, da kuma mara baya ga huldar kasa da kasa da MDD.

Baya ga haka, kungiyar ta ce ya kamata MDD ta ci gaba da karfafa kulawa da tsara kasafin kudin da inganta tafiyar da shi da tabbatar da an yi amfani da dukkan kudaden da mambobin majalisar suka bayar ta hanyar da ta dace. (Fa’iza Mustapha)

Tasal