logo

HAUSA

Jami‘in MDD ya yi Allah wadai da harin da Boko Haram ta kai kan cibiyoyin bayar da agajin jin kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya

2021-04-13 12:53:45 CRI

Jami’in kula da harkokin tsare-tsare da ayyukan jin kai na MDD dake Najeriya Edward Kallon, ya yi Allah wadai da harin da mayakan Boko Haram suka kai kan fararen hula da ma cibiyoyin bayar da agaji masu tarin yawa a karshen mako a garin Damasak na jihar Borno, jihar da ta shafe sama da gwamman shekaru tana fama da hare-haren mayakan na Boko Haram.

Rahotanni daga yankin na cewa, harin da mayakan suka kai, ya shafi daya daga cikin cibiyoyin bayar da agaji dake karkashin kulawar MDD, lamarin da ya haddasa mutuwar fararen hula da sojoji da dama.

Wata sanarwa da jami’in na MDD dake Najeriya ya aikawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa, ya yi bakin cikin samun labarin kai hare-haren da ma yadda aka bankawa kayayyakin cibiyoyin bayar da agaji wuta ba. Ya ce ya damu matuka game da sake samun rahotanni kai hare-haren tashin hankali da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai ke kaiwa, wanda ke cusa rayukan fararen hula cikin hadari.

A cewar jami’in, an auna wasu cibiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa guda uku ne dake a garin Damasak, inda aka lalata tare da banka musu mutu da ya rika ci, tun daga ranar Asabar da dare har zuwa wayewar garin Lahadi.(Ibrahim)