logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a hada hannu wajen shawo kan abubuwan da kiyayya ke haifarwa

2021-04-08 14:37:39 CRI

MDD ta yi kira da a hada hannu wajen shawo kan abubuwan da kiyayya ke haifarwa_fororder_210408-Rwanda

Yayin da duniya ke tunawa da kisan kare dangi da ya auku a Rwanda a shekarar 1994, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a hada hannu wajen shawo kan kiyayya domin kaucewa maimaituwar tarihi.

A sakonsa domin ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Tutsi a Rwanda, Sakatare Janar din ya ce ya zama wajibi kowa ya yi wa yanayin da ake ciki a duniya yanzu, duba na tsanaki tare da tabbatar da an dauki darasi daga abun da ya faru shekaru 27 da suka gabata. (Fa’iza Mustapha)