logo

HAUSA

Guterres ya yi kira da a dauki matakai 6 don farfado da kasashe daga tasirin COVID-19

2021-04-13 12:56:55 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a dauki matakai guda 6, a wani mataki na taimakawa kasashe farfadowa daga tasirin annobar COVID-19, har ma su dawo kan ganiyarsu na cimma manufofin ci gaba mai dorewa na MDD (SDGs).

Guterres wanda ya bayyana haka yayin bude taron dandalin tattalin arziki da jin dadin jama’a na shekarar 2021, game da harkokin kudi da raya kasa, ya bayyana cewa, manufar samar da kudade don raya kasa sakamakon annobar COVID-19, ita ce, kara kokarin samar da albarkatu da kuduri na siyasa. Yana mai cewa, tun barkewar wannan annoba shekara guda da ta gabata, har yanzu babu wani hadin gwiwar bangarori da ya yi tasirin da ake fata.

A don haka, jami’in na MDD ya ba da shawarwari guda 6, da suka kamata a mayar da hankali a kansu, domin magance wannan kalubale. Na farko wajibi ne a samar da alluran riga kafi a dukkan kasashe. Na biyu, akwai bukatar a sauya tsarin da cimma na samar da kudade, ciki har da kasashe masu matsakaicin kudaden shiga. Na uku, akwai bukatar a yi amfani da kudaden da aka tara a wuraren dake da mutakar bukatarsu.

Shawara ta hudu a cewar Guterres, ita ce akwai bukatar dakatar da bashin da ake bin wasu kasashe, da yi musu sassauci, da samar da kudade ga kasashen dake bukatar hakan. Sai na biyar, bukatar zuba jari a bangaren al’umma. Kana na shida, akwai bukatar a sake dawo da harkokin tattalin arziki sannu a hankali, bisa manufofin samun ci gaba da mai dorewa na MDD da kuma yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris.(Ibrahim)