logo

HAUSA

Uganda ta bukaci al’ummar musulmin kasar su kiyaye matakan kandagarkin COVID-19

2021-04-14 11:06:31 CRI

Uganda ta bukaci al’ummar musulmin kasar su kiyaye matakan kandagarkin COVID-19_fororder_非洲疫情2

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya bukaci al’ummar musulmi a kasar, su ci gaba da kiyaye matakan kandagarkin cutar COVID-19 yayin da suke azumtar watan Ramadan.

Cikin sakon da fadar gwamnatin kasar ta fitar, shugaba Museveni ya bukaci al’ummar su yi salloli a gida domin kaucewa taruwa.

Sai dai ya ce wadanda ke kiyaye matakan kandagarkin cutar, kamar na ba da tazara da tsafta, za su iya sallah a masallatai.

Ya kuma yi kira a gare su, da su yi addu’o’in neman zaman lafiya da ci gaban kasar, tare da fatan a karshen watan Ramadan, addu’o’i da ibadunsu za su karbu tare da samun lada.

Alkaluman ma’aikatar lafiya ta kasar ta nuna cewa, gwaje-gwajen da aka yi a ranar 11 ga wata, sun tabbatar da samun sabbin mutane 30 da suka kamu da cutar, wanda ya kawo jimilar wadanda suka kamu a kasar zuwa 41,204. Kana mutane 40,779 sun warke daga cutar, yayin da ta yi ajalin mutane 337. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha