logo

HAUSA

Jami’in jam’iyyar Uganda: Salon mu’amalar da Sin ke yi da kasashen Afrika muhimmi ne

2021-04-11 16:10:32 CRI

Jami’in jam’iyyar Uganda: Salon mu’amalar da Sin ke yi da kasashen Afrika muhimmi ne_fororder_0411-Afirka-Uganda-2

Richard Todwong, mataimakin babban sakataren jam’iyyar National Resistance Movement party, NRMP mai mulkin kasar Uganda, ya bayyana cewa, a halin yanzu, za a iya tuka mota daga wannan yanki zuwa wancan a kasar Uganda akan ingantattun titinan mota, mafi akasarinsu kamfanonin kasar Sin ne suka gina su.

A wata zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan, Todwong ya ce, shawarar “Ziri daya da Hanya daya” ta taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki, kasancewar tana sada al’ummu daban daban da juna, kuma wannan na daya daga cikin alfanun dake tattare da shawarar, in ji mista Todwong.

Ya ce, shugabancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin CPC, tana da hangen nesa wajen kyautata mu’amalarta da kasashen Afrika har ma da sauran kasashe masu tasowa, jami’in ya kara da cewa, salon da kasar Sin ke amfani da shi wajen huldarta da kasashen Afrika muhimmi ne, mai dorewa, kuma sahihi ne.

Ya ce a mafi yawan kasashen Afrika, musamman kasashen kudu da hamadar sahara, akwai ayyukan more rayuwa masu tarin yawa wadanda kasar Sin ke gudanarwa. Tana gina madatsun ruwa, da gina hanyoyin mota, kana tana fadada ayyukan samar da lantarki a yankunan karkara.(Ahmad)

Bello