logo

HAUSA

Uganda ta dakatar da kaddamar da bututun mai saboda makokin shugaban kasar Tanzania

2021-03-24 10:21:36 CRI

Mahukuntan kasar Uganda, sun sanar da dage lokacin kaddamar da aikin gina sabon layin bututun man fetur na EACOP, wanda zai hade kasar da gabar tekun Tanzaniya, saboda nuna alhinin rasuwar shugaban Tanzania John Magufuli.

Wata sanarwa da kamfanin mai na Uganda PAU ya fitar, ta ce marigayi shugaba Magufuli, ya taka muhimmiyar rawa wajen fitar da shirin aikin mai matukar fa’ida ga kasashen biyu. Kuma saboda da makokin rasuwarsa, an amince da dage kaddamar da aiki zuwa wata mai zuwa.

Tsayin bututun man dai ya kai kilomita 1,445. Ya kuma hade rijiyoyin mai dake yammacin Uganda zuwa tashar tekun Tanga dake Tanzania.  (Saminu)