logo

HAUSA

Uganda ta yabawa Sin bisa taimaka mata a yaki da COVID-19

2021-04-01 11:22:53 CRI

Uganda ta yabawa Sin bisa taimaka mata a yaki da COVID-19_fororder_210401-Uganda

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres a jiya Laraba ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a jamhuriyar Nijer bayan wani yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren ya ce, Guterres ya nuna matukar damuwa bayan bibiyar halin da ake ciki a kasar. Sannan ya bukaci dukkan masu hannu a wannan yunkuri da su guji aikata duk wani abin da zai iya zama barazana ga tsarin demokaradiyya da zaman lafiyar kasar. Ya kuma yi kira musamman ga sojoji da su yi kokarin sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar ya dora musu.

Babban sakataren ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a jamhuriyar Nijer da su mutunta manufofin tsarin demokaradiyya su amince da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 21 ga watan Fabrairu a zagaye na biyu kuma su bayar da cikakkiyar damar mika mulki ga sabuwar gwamnatin kasar cikin kwanciyar hankali. (Ahmad)